Yadda aka kama ɗan bindiga ɗauke da N13m da bindigogi a hanyar Jos
Published: 12th, July 2025 GMT
Sojoji sun kama wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane ɗauke da tsabar kuɗi Naira miliyan 13 a kan hanyar Kaduna zuwa Jos a Jihar Kaduna.
Dakarun Rundunar Operation Safe Haven sun kuma ƙwace bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da harsasai 30 a hannun ɗan ta’addan a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.
Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya ce dubun ɗan ta’addan ta cika ne a wani shingen bincike da ke yankin Agameti a kan babbar hanyar Wamba zuwa Jos.
Manjo Zhakom ya ce a ranar Laraba, sojoji suka tsayar da wata mota ƙirar Volkswagen Golf da ke ɗauke da mutum uku, amma kafin ta ƙaraso inda za ta tsaya, biyu daga cikin mutanen suka fice suka tsere.
Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu MusawaYa bayyana cewa sojojin sun gano ramin harbin bindiga da kuma jini a jikin motar, kuma direban ya yi yunƙurin ba su cin hanci amma suka ƙi karba.
“Suka kama shi, bayan cikar wanda ake zargin da kuma cikin motar suka gano bindigogi biyu ƙirar AK-47 da harsasai 30 da wayoyi guda uku da layu da tsabar kuɗi N13,742,000, da wuƙa da sauransu.
“A yayin bincike ya amsa cewa yana da hannu garkuwa da mutane a kan hanyar Jos zuwa Makurɗi, kuma ya amince ya kai sojoji maɓoyarsa.
“A yayin da suke tafiya, wanda ake zargin ya yi yunƙurin ƙwace makamin jami’anmu, amma suka murƙushe shi” in ji shi.
Manjo Zangon ya ce rundunar na ci gaba da zurfafa bincike domin kamo sauran ’yan ta’addan da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane Harsasai
এছাড়াও পড়ুন:
Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya ta buƙaci Majalisar Tarayyar da ta amince da ƙudirin dokar da zai ba ta damar bincikar ɗaiɗaikun ’yan Najeriya game da yadda suka tara dukiyarsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito Shugaban EFCC, Ola Olukayode yana cewa ƙudirin mai suna “Unexplained Wealth Bill” ya je gaban ’yan majalisar tun a majalisa ta tara, wanda suka yi watsi da shi.
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba“Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɓarnar da ake yi arzikin ƙasarmu da kuma matsalar tsaro,” a cewarsa yayin wani taro da kwamatocin majalisar tarayya suka shirya kan arzikin ƙasa.
“Idan kana bincikar ayyukan ’yan fashin daji, da ta’addanci, za ka ga suna da alaƙa da wani nau’i na cin hanci da rashawa, ko kuma karkatar da kuɗaɗen da suka kamata a yi wa al’umma aiki.
“Ina neman ku taimaka min wajen amincewa da ƙudirin “Unexplained Wealth Bill”. Shekara ɗaya kenan ina neman hakan, kuma shi ne dai majalisa ta tara ta yi watsi da shi. “Idan ba mu binciki dukiyar da mutane suka tara ba ba za mu taɓa gyara al’amuran ba.
“Akwai wani da ya yi aiki shekara a wata ma’aikata. Mun lissafa baki ɗayan albashi da alawus ɗinsa. Sai kuma muka gano gidaje biyar da yake da su, biyu a Maitama, uku a Asokoro. Amma kuma ana so mu gabatar wa kotu hujja a kansa kafin mu yi wani bincike. Wannan abin takaici ne.”