Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kama ‘Yan Leken Asirin Isra’ila A Lardin Mazandaran Na Kasar Iran
Published: 12th, July 2025 GMT
Dakarun juyin jaya halin Musulunci ta Iran sun kama wani wakilin hukumar leken asirin Isra’ila Mossad a arewacin kasar Iran
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanar da kame wani jami’in hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila “Mossad” a lardin Mazandaran (arewacin kasar Iran), wanda ke shirin kai harin ta’addanci a cikin kasar.
Sanarwar da dakarun kare juyin juya halin suka fitar ta bayyana cewa: wani ma’aikacin fage na makiya da ke shirin aiwatar da ayyukan ta’addanci ta hanya kai tsaye wajen jagorantar masu adawa da Iran a kasashen waje, an kama shi ne a wani gagarumin samame da jami’an leken asirin na Karbala suka kai, kafin ya aiwatar da duk wani aikin ta’addanci.
Sanarwar ta kara da cewa: Bincike ya kai ga gano tare da kama wasu da dama daga cikin ‘yan kungiyar leken asirin da lamarin ya shafa.
Tawagar masu leken asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci a lardin Mazandaran ta tabbatar da cewa tana cikin shiri da kuma taka tsantsan, kuma ta yi gargadin cewa “duk wani mataki na nuna adawa da tsaron kasar, zai fuskanci dauki mai tsauri da raɗaɗi.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Aref Ya Bayyana Cewa: Iran Ba Ta San Kalmar Mika Wuya Ba A Al’adunta Da Tsaronta
Mataimakin shugaban kasar na farko ya jaddada cewa: Kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Iran
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: kalmar mika wuya ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron kasar.
Arif ya ce: Kamar yadda kuke gani kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa, su mutane ne masu wayewa, tare da ingantaccen tarihin al’adu wanda ya wuce dubban shekaru. Ba su neman yaki, kuma ba su fara shi ba. Sun yi imani da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma a shirye suke don tattaunawa, amma ba za su mika wuya a kowane hali ba.
A wata hira da ya yi da KHAMENEI.IR, Aref ya jaddada cewa: An sha ambaton hakan, sannan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa ba za mu fara yaki ba, amma idan aka tsokani Iran, to Iran zata mayar da martani, kuma haka yake har yanzu. Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba za a taba amince da su ba. An dai tsagaita bude wuta a kasar Labanon, amma kamar yadda ake gani bayan tsagaita wuta an samun adadin shahidai masu yawa. Sadaukarwarsu ta kasance domin kare Iran ce.