NPA Ta Tarbi Babban Jirgin ‘Ruwa MB Ocean Dragon’ Don Bunkasa Ayyukanta
Published: 11th, July 2025 GMT
An tsara Jirgin zai rinka yin zirga-zirga ne, zuwa daukacin kasashen da ke Afirka ta yamma da kuma sama da haka, musamman yin zirga-zirga daga Nijeriya zuwa kasashen, Jamhiriyar Benin, Togo, Ghana, Kamaru, Sierra Leone, Ibory Coast, Masar, Afirka ta Kudu da sauransu, tare da kuma nuna bukatar yin kasuwanci wadda tuni, aka fara ta.
A martaninsa kan wannan nasarar, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, “ Wannan nasarar ta nuna irin mayar da hankalin da NPA ke ci gaba da yin a kara bunkasa ayyukan Hukumar wanda ta zo daidai da ta irin ma’aikatar bunkasa tattalin arzikin kasa.
A na ta bayanain Mataimakiyar Shugabar kamfanin na On her Clarion Shipping West Africa Limited, Bernadine Eloka, ta bayyana cewa, jigilar kaya a cikin Jirgin a Tekunan ruwan Nijeriya da kuma kokarin kara karfafa hada-hadar kasuwanci a Afrika ta yamma, za ta taimaka matuka wajen kara habaka kasuwanci.
Ta ce, manufar kamfanin shi ne, ya kara samar da saukin yin hada-hadar zirga-zigar kaya a tsakanin kasashen Afirka, musamman ta hanyar bude sabon babin kasuwanci a Tashoshin Jirgan Ruwa na Nijeriya da kasashen, Ghana, Ibory Coast da kuma sama da haka.
“Mun samar da Jirgin na MB Ocean Dragon ne, domin mu samar da saukin ga yin jigilar Kwantainoni, mai makaon yin jigilarsu, a kan tituna,” Inji ta.
Ta ci gaba da cewa, mai makon a rinka shan wahala wajen yin jigilar Kwantainoni a cikin manyan motoci daga Tashar Jirgin Ruwa ta Lekki zuwa ta Onitsha, Fatakwal, ko kuma Kalaba, Jirgin na Dragon, zai iya dakon Kwantainonin da suka kai yawan 349 ya kuma kaisu, Tashar Jirgin Ruwan da ka tsara za a kaisu, a cikin kwana biyu.
A cewarta, wannan Jirgin zai kuma taimaka wajen kara karfin guiwar sauran masu zuba hannun jari a fanin, samar da ayyukan yi da kuma rage dogaro kan Jiragen Ruwa na ketare.
Shi kuwa Manajin Darakta na mai kula da sashen kaya na kamanin Mustafa Mohammed, ya bayyana cewa, kamfanin ya mayar da hankali wajen yin gasa da sauran manyan kamfanonin kasashen duniya kamar su, Maersk Line da MSC, wanda hakan ya sanya, kamfanin ya fara turo Jirginsa na MB Ocean Dragon, zuwa cikin Nijeriya, musamman domin ya zuba hannun jarinsa a fannin sufurin Jiragen ruwan kasar.
Ya ci gaba da cewa, tuni kamfanin ya samu wasu kamfanoni da ke bukatar a yi masu dakon Kwantainoni guda 1,300, musamman wasu manoma da ke son ayi masu jigilar amfanin gona da kuma wasu masana’antu da ke bukatar a yi masu jigilar kayan da suka sarrafa, domin kar su su samu jinkirib, da zai haifar masu da yin asarar kayansu.
Kazalika, wannan ci gaban dai, na zuwa ne, daidai da sanarwar da Shugaban NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya yi, na zuba dala miliyan 60 a matsayin sabon hannun jari, domin a kara samar da huddar cinikayya, ta kara bunkasa harkokin kasuwanci a Tashoshin Jiragen ruwa na kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.
Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA