Leadership News Hausa:
2025-07-11@18:26:30 GMT

Gwamnan Zamfara Ya Raba Buhunan Taki 59,205 Ga Manoman Jihar

Published: 11th, July 2025 GMT

Gwamnan Zamfara Ya Raba Buhunan Taki 59,205 Ga Manoman Jihar

Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka raba sun haɗa da irin shinkafa kilogiram 34,800, irin masara kilogiram 80,000, da lita 23,740 na maganin ciyawa, lita 11,735 na maganin kwari, da buhunan sinadarai na gyaran iri 23,470.

 

A yayin jawabin maddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon takin zamani kyauta na nuni da yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin kawo sauyi a jihar Zamfara ta hanyar noma mai ɗorewa da bunƙasa karkara.

 

Ya ce, “Aikin noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jiharmu, ba sashe kaɗai ba ne, amma asalin al’ummarmu ne.

 

“Gwamnatinmu ta rungumi taken ‘noma abin alfaharinmu ne’. Noma na nuna ainihin ko su wane ne mu da kuma abin da ya kamata mu ba da fifiko a matsayinmu na al’umma, sama da kashi 85 na al’ummarmu sun dogara ne kan noma don rayuwa. Haƙƙin ne a kan mu, kuma haƙiƙa ya zama wajibi mu ba su goyon baya da ƙarfafa su.

 

“Wannan gwamnatin tana kallon noma a matsayin dabarar samar da abinci, samar da ayyukan yi, rage fatara, da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya, shi ya sa muke aiwatar da shirin kawo sauyi a fannin noma, wanda ya dace da buƙatun al’ummominmu da kuma yin daidai da manufar ci gaba mai ɗorewa ta 2, wanda ke neman kawo ƙarshen yunwa, inganta abinci mai gina jiki, da bunƙasa noma mai ɗorewa.

 

“Duk da ƙalubalen sauyin yanayi da kuma ƙarshen lokacin damina na 2025, mun ci gaba da mai da hankali sosai, gwamnatinmu tana tallafa wa manoma da kayan aikin da ake buƙata don bunƙasa noma da samun kuɗin shiga, muna saka hannun jari a fannin samar da iri, takin zamani, fasaha, da jarin bil’adama don samun tasiri na dogon lokaci.

 

“Manufarmu ta haɗa da ƙarfafa mata, matasa, da kuma ɗaiɗaikun mutane masu buƙatu na musamman a matsayin wakilai na kawo sauyi, ba wai mahalarta kaɗai ba. Mun bullo da ingantaccen tsarin rabo cikin gaskiya don tabbatar da cewa tallafin ya isa ga manoman da suka dace a daidai lokacin da ya dace.

 

“Mun gane cewa manoma na fuskantar matsaloli kamar rashin damar samun kayan aiki, kuɗaɗe, rashin tabbas na kasuwa, asarar bayan girbi, da kuma tasirin sauyin yanayi. Amma muna tunkarar waɗannan batutuwa.

 

“Ta hanyar shiga tsakani, muna gina tsarin da zai taimaka wa manomanmu daga shuka har zuwa bayan girbi. Muna haɓaka noma da injinan zamani.

 

“Bari na dan ɗauki lokaci in yi magana kai tsaye ga waɗanda suka ci gajiyar shirin na bana. Waɗannan kayayyakin ba na sayarwa be ne. Ba kayayyakin da za a yi ciniki da su ba ne domin a samu ci gaba cikin gaggawa. Kayan aiki ne na samar da ci gaba, zuba jari a nan gaba da kuma makomar Zamfara. Ku yi amfani da su cikin hikima, ku yi amfani da su cikin gaskiya, ku bar su su zama ginshiƙi na ƙaruwar girbi da inganta rayuwa.

 

“Baƙin alfarma, ’yan uwa maza da mata, yanzu ya zama abin alfaharina na ƙaddamar da shirin Rarraba Kayayyakin Aikin Noma na 2025 a hukumance, wanda zai amfani ƙananan manoma 59,205 a faɗin jihar mu.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari

 

A daya bangaren kuma

Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; wadannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma hadari duk da ke dauke cikin wannan labari.

Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna fuskantar kalubale na yi wa al’umma aiki ta hanyar samar da damammaki, rage talauci da kuma tsantseni wajen sarrafa dukiyar al’umma.

Duk da cewa, har yanzu akwai sauran rina a kaba, amma abin da na gani a dan wannan lokaci da na ziyarci wadannan jihohi uku, tattakina zuwa Jihar Zamfara; shi ne mafi matukar tsoro a wajena

 

Zuwa Gusau

A karon farko da aka gayyace ni zuwa babban birnin jihar, Gusau, sai na yi watsi da tafiyar. Domin kuwa, a tafiya irin wannan akwai bukatar yin tunani da nazari mai zurfin gaske, musamman ganin yadda nake samun munanan labarai a kan Ado Aliero da sauran tawagarsa ta ‘yan ta’adda da ke yankin.

Har ila yau, sai aka sake turo min da wata gayyatar. Amma dai, a wannan karon akwai dan kwarin gwiwa, musamman ganin cikin tawagar da zan bi na tattaunawa ta farko da za a yi da Gwamna Dauda Lawal kai tsaye a kan wa’adin shekaru biyu da ya kwashe kan mulki. Tawagar ta kunshi; Gbenga Aruleba daga gidan talajin na AIT, Reuben Abati, ARISE TB da matarsa, Kiki, sai Ahmed Shekarau daga Media TRUST, Onuoha Ukeh daga SUN da kuma Babajide Otitoju, wanda Olajumoke Olatunji ya maye gurbinsa daga TBC.

 

ChatGPT da Gusau

Amma fa akwai matsala. Ta yaya za mu isa Gasau, duk da sanin abin da muka sani, na tambayi ‘ChatGPT’. Sai amsa min da cewa, kada ku tafi idan har tafiyar ba mai muhimmanci ba ce.

Ya ba da sanarwar tafiye-tafiye daga ofishin harkokin waje na burtaniya, Australia, Canada da kuma Amurka tare da gargadi game da tafiye-tafiye saboda tashin hankali, ta’addanci da kuma garkuwa da mutane, yana mai bayyana cewa; “Babbar matsaya daga hukumomin kula da tafiye-tafiye, ba ta ba da shawarar yin tattaki zuwa Jihar Zamfara, idan har ba akwai bukatar yin hakan ba.

“Titin Zariya zuwa Zamfara, musamman Funtua da ke Jihar Katsina, Tsafe, Maru-Dansadau, an bayyana su a matsayin wasu yankuna na mutuwa, wato wani filin wasa ne na Dogo Gide da Bello Turji, wanda tawagarsu ta ‘yan ta’adda suka kashe matafiya akalla 20, kamar yadda rahoton AP ya bayyana a watan Afrilun wannan shekara. Ina kan hanya, amma na kudiri niyyar tafiya.

 

Mutuwa da dawowa

Na yi ta mutuwa ina dawowa a cikin awa biyu da minti sha biyar, tsoro ya gama kama ni tare da alhinin cewa; idan na mutu a shekara 60, ba wai na mutu da kuruciya ba ne. Ban san cewa, matata ta lallaba ta sanya min wani abin kariya a cikin wata ‘yar karamar kwalba.

Gaba-daya ban lura ba, sai da na dawo daga tafiyar ina goge jakata, wannan ya isa ta bugi kirji da cewa; ta taimaka min da wani sirri na kariya. Na kasance a ankare cikin tsawon wannan tafiya ta kimanin kilomita 450 daga Abuja, cike da dimuwa.

Abin da ya ba ni mamaki, titin da ke tsakanin Zaiya da Katsina, mai layi biyu ne, sannan kuma yana da kyau sosai; titin bai tsuke ba sai da muka shiga Katsina, kana kuma ya sake bude bayan mun yi nisa ga duwatsu masu ban sha’awa da tsaunika da dukkanin bangarorin titin biyu. Amma titin Abuja zuwa Kaduna, abin kunya ne idan aka kwatanta shi da wannan, amma duk da haka; babban titin Abuja zuwa Kadunan ya lalace, kai ka ce shi ne kofar shiga Arewa Maso Yamma.

 

Fargaba da dimuwa…

Bayan Zariya, a wasu lokuta, mun wuce garuruwa masu yawan jama’a, amma mafi shahara a cikinsu shi ne garin Funtua, garin wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa da suka hada da marigayi Malam Ismail Funtua da kuma fitaccen dan kasuwa, Umaru Mutallab.

Kowa ya yi tsit, kuma na kasa tambayar kaina cewa; ko mutanen da ke zaune a kauyukan da kananan garuwan da muke ratsawa, sun san abin da ake fada game da su kafafen yada labarai? Yayin da muka shiga Tsafe, garin daya daga cikin manyan ‘yan ta’addan da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane, wadanda suka samu nasarar share wajen zama a Jihar Katsina kafin ziyarar tamu, duk gashin da ke jikina sai da ya tashi.

Duk da cewa, mun samu rakiyar jami’an ‘yansanda ga kuma shingayen sojoji da dama a hanyar, yayin da muka isa Tsafe, kilomita 48 zuwa Gusau, ba ku ga irin tsoro da firgicin da ke cikin motarmu ba. shiru kake ji kowa ya yi dif.

Bayan Tsafe, na yi zaton tashin hankali ya kare a wannan tafiya. Sai kuma na ji na samu sauki tare kuma da shiga rudani da muka shiga Gusau. Saukin shi ne da muka isa lafiya, rudanin kuma saboda titi mai hannu biyu da ake dab da kammala, wanda ya hade da na Zamfara mai tattare da hadari da ban tsoro a tare da shi.

 

An samu canji

Ashe da rabon zan ga irin wadannan al’amuran a Enugu, inda rabo da zuwa tun

2006 (lokacin Chimaroke Nnamani yana gwamna). Ziyarar da na yi zuwa Zamfara na yi ta tun a farkon shekarun 1990, lokacin tana hade da Jihar Sakkwato

 

Jiha

Bayan wani Kantoman Mulkin Soji daya, da kuma wasu gwamnonin farar hula hudu, kafin Dauda, na biyar, Zamfara ta kasance wani abu kamar tallan shirin wasan kwaikwayo na Kannywood, inda ‘yan siyasa ke kwashe dukiyar kasa, ciki har da jama’arta, tare da nuna iko ko shakka babu Dauda zai iya nuna bambanci a wannan tsari. A cikin shekaru biyu, ya inganta asibitocin tuntuba da ke Gusau zuwa asibitin koyarwa mai dauke da wasu kayan aiki na zamani, ya kuma inganta harkar samar da ruwan sha, sannan ya kawar da koma bayan kudin WAEC da NECO na dalibai, lamarin da ya sa jihar ta kasance da ta samu kyakkyawan sakamako na tsawon shekaru. Haka kuma ya gina sabon filin jirgin sama wanda za a iya budewa kafin Satumba.

Gwamnati ta ce ta biya basussukan gratuti da kuma fansho ga ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha tun daga shekarar 2011, da aka kiyasta kudin sun kai Naira biliyan 13.6, baya ga biyan bashin albashin watanni hudu da ya gada tare da kara mafi karancin albashi daga Naira 7,000 duk wata zuwa Naira 70,000.

 

“Komawar harkoki”

A lokacin da ake tattaunawar kai tsaye da Abati ya tambayi Dauda yadda ya sanya jihar a kan turba mai ban sha’awa, ciki har da ba ta wutar lantarki ta farko tun bayan da aka kirkiro ta shekaru 29 da suka gabata, gwamnan ya ce hakan ya faru ne ta hanyar toshe leken asiri ta hanyar amfani da fasaha, da kuma ba da fifiko wajen bunkasa albarkatun jama’a da kuma inganta karfinsu.

Ya ce an kuma yi amfani da fasaha don tattarawa da yin amfani da bayanan sirri don gina jiha mafi aminci, yana mai shan alwashin cewa ba za ai yi sulhu da ‘yan fashi da masu laifi ba.

Idan rayuwar dare ta daidaita a Gusau, babu shakka dukkan jama’ar da suka rasa matsugunai da wuraren sana’a za su dawo inda suke musamman gonaki a hankali. Wannan kuma wani hangen nesa ne da mutum zai iya duba jihar da aka ayyana kusan shekaru talatin ta hanyar cusa tsattsauran ra’ayi na addini, sata da kuma ‘yan fashi.

Ishiekwene Babban Editan LEADERSHIP kuma mai Rubuce-rubuce a Kafofin watsa labarai da harkokin Kudi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Magance Matsalar Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta: Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyarwa A Makarantun Jihar
  • Jihohi 10 Sun Kinkimo Bashin Naira Biliyan 417 Duk Da Karin Samun Kudaden Shiga
  • Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyar Da Ɗalibai A Makarantun Zamfara
  • Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari
  • Kotun ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin gwamnan Edo
  • Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo a Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo
  • Har Yanzu A Cikin PDP Nake, Ba Zan Koma APC Ko ADC Ba – Gwamnan Zamfara
  • UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
  • Har Yanzu Cikin PDP Nake, Ba Zan Koma APC Ko ADC Ba – Gwamnan Zamfara