Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC
Published: 11th, July 2025 GMT
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya ta buƙaci Majalisar Tarayyar da ta amince da ƙudirin dokar da zai ba ta damar bincikar ɗaiɗaikun ’yan Najeriya game da yadda suka tara dukiyarsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito Shugaban EFCC, Ola Olukayode yana cewa ƙudirin mai suna “Unexplained Wealth Bill” ya je gaban ’yan majalisar tun a majalisa ta tara, wanda suka yi watsi da shi.
“Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɓarnar da ake yi arzikin ƙasarmu da kuma matsalar tsaro,” a cewarsa yayin wani taro da kwamatocin majalisar tarayya suka shirya kan arzikin ƙasa.
“Idan kana bincikar ayyukan ’yan fashin daji, da ta’addanci, za ka ga suna da alaƙa da wani nau’i na cin hanci da rashawa, ko kuma karkatar da kuɗaɗen da suka kamata a yi wa al’umma aiki.
“Ina neman ku taimaka min wajen amincewa da ƙudirin “Unexplained Wealth Bill”. Shekara ɗaya kenan ina neman hakan, kuma shi ne dai majalisa ta tara ta yi watsi da shi. “Idan ba mu binciki dukiyar da mutane suka tara ba ba za mu taɓa gyara al’amuran ba.
“Akwai wani da ya yi aiki shekara a wata ma’aikata. Mun lissafa baki ɗayan albashi da alawus ɗinsa. Sai kuma muka gano gidaje biyar da yake da su, biyu a Maitama, uku a Asokoro. Amma kuma ana so mu gabatar wa kotu hujja a kansa kafin mu yi wani bincike. Wannan abin takaici ne.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazanar Sa Ga Nijeriya
Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa.
“Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in ji shi.
A ƙarshe, yayi kira ga ƴan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da juriya, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata a fifita zumunci fiye da rarrabuwar kai.
“Yan uwa ƴan Nijeriya, lokaci ne da muke buƙatar haɗin kai fiye da komai. Allah ya taimaki Nijeriya,” in ji Kwankwaso.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA