2025-07-12@12:18:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11
«ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan»:
Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba da goyon baya wajen raya masana’antu, da habaka tsare-tsaren tattalin arziki a Afirka. Dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da ci gabanta da kasashen Afirka na bai daya, shi ne domin ra’ayinta game da dangantakar dake tsakaninta da Afirka, wato al’ummar Sin da Afirka suna da makomar bai daya a nan gaba. A ganin kasar Sin, ita da Afirka suna da tarihi...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas. Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar. Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Fubara, ya samu saɓani da ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan hauwansa mulki. Saɓani kan ikon mallakar kuɗin jihar da naɗin muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar. A watan Maris 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya. Ya naɗa...
“Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da suka kamata tun lokacin da aka kaddamar da dokar ta bacin.An horar da Malaman makarantun gwamnati,ana kuma ci gaba dayin hakan. “Saurin biyan kudaden bashi da Hukumomin WAEC da NECO ya kawo kwanciyar hankali ga daliban da suka kammala makaranta da rubiuta jarabawa, sai dai basu samu ci gaba da karatu ba saboda Hukumomin jarabawar sun rike masu sakamakon jarabawar da suka yi. Daga...
“Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne. “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.” Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi. Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba...
Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025. Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar. UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar da Siriya daga cikin sahun masu fada da makirce-makircen yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ta hanyar kulla kyakkyawar alaka da su, da janyewa daga duk hakkokin kasar Siriya da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta mamaye na Siriya a baya-bayan nan. Manufar samar da sabuwar gwamnatin masu da’awar jihadi, kamar yadda aka sani, ita ce tabbatar da tsaron babban sansanin Amurka mafi girma a yanking abas ta tsakiya,...
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya. Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas...
Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya ziyarci Cibiyar Horar da Sojoji da ke Zariya, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin kayan aiki da ci gaba da inganta horon kuratan sojoji domin su dace da buƙatun zamani. A lokacin ziyarar, Ministan ya bayyana gamsuwarsa da horon da kurata na kashi 88 ke samu, inda ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na bunƙasa kayan horo da samar da ingantattun makamai da kayan aiki ga dakarun sojoji. Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Badaru ya yi alƙawarin tuntuɓar Gwamnatin Jihar Kaduna, domin kammala ginin Makarantar Sakandaren Chindit, wadda ba a kammala ta ba tsawon lokaci. Ya kuma bayar da tabbacin...
Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki. Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa musamman a lokacin azumin Ramadan, a wata tattaunawa da suka yi da gidan rediyon Najeriya, sun bayyana rashin jin dadinsu da tashin gwauron zabi. ‘Ya’yan itatuwa na da matukar muhimmanci ga lafiyar mu a lokacin azumi, amma farashin na kara zama wanda ba zai iya jurewa ba,” in ji su. Malam Ado Shehu, jami’in hulda da jama’a na kasuwar ‘ya’yan itacen Naibawa,...
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa. Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa. Guterres ya ce ya ji dadin matuka bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis. Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba...