Sudan : Janar al-Burhan Ya Shelanta ‘yantar Da Birnin Khartoum
Published: 27th, March 2025 GMT
Babban hafsan sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya shelanta ‘yantar da Khartoum Babban birnin kasar.
Wannan na zuwa ne bayan da tun da farko ya sanar da cewa dakarunsa sun kwato filin jirgin saman babban birnin, wuri mai matukar mahimmanci daga hannun dakarun ‘yan tawaye na RSF.
“An ‘yantar da Khartoum, an gama,” in ji shugaban na Sudan daga fadar shugaban kasa a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na kasar.
Kazalika, wata sanarwa da sashen watsa labarai na majalisar rikon kwarya mai mulkin kasar ta fitar, ta ce Al-Burhan ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Khartoum ta jirgi mai saukar ungulu a jiyan, jirgin da ya zamo na farko da ya sauka a filin, tun bayan barkewar tashin hankali a watan Afrilun shekarar 2023.
Daga nan ne kuma ya duba sassan rundunar sojin gwamnati dake tsaron filin jirgin kafin ya wuce zuwa fadar gwamnati.
Tun daga farkon shekarar 2024, dakarun sojin gwamnati na SAF ke ta kwace sassan kasar daban daban, musamman a birnin Omdurman na arewacin Khartoum, inda suka kwace kaso mai yawa na birnin, lamarin da ya karfafa ikonsu sama da na dakarun RSF a yankin.
A ranar Juma’a data gabata, sojojin na sudan sun ayyana kwace iko da fadar gwamnati, da wasu muhimman ofisoshin gwamnatin kasar dake Khartoum, wuraren da a baya suka kasance muhimman sassa da dakarun RSF ke rike da su a birnin na Khartoum.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Mamayar Isra’ila Kan Kasar Yemen
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen
Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada goyon bayansu ga shugabancin kasar da sojojin kasar da kuma al’ummar kasar ta Yemen.
Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa: “Kazamin harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yamen, wanda ya shafi kayayyakin more rayuwa na fararen hula da tashoshin wutar lantarki da tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Ras Issa da kuma Salif, wani sabon laifi ne na ha’inci da ya kara yawan muggan laifukan ‘yan mamaya a yanki.”
Sanarwar ta kara da cewa: Wannan mummunan wuce gona da iri na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Yemen da dakarunta ke samun nasarori a jere wajen karya martabar makiya ‘yan sahayoniyya da kutsawa cikin zurfin dabarun na yaki da kuma kafa madaidaicin matakin da ya dace wanda ke nuna ‘yancin kai na mutanen da ba su san yadda za su ja da baya ba.