Sako daga Aminu Murtala Jihar Kano:
Ina gaishe da malamaina na Islamiyya dana boko kamar irinsu; Mr Bilyaminu Ogamba, Mr Alkali Nok, Mr Piter Aondo, Mr Mahmud Tanko Yakasai, Mrs Zainab Mrs. Modupe Balogun Mrs. Aisha Goro, Mr. Ibrahim, Mrs. Mary, Mrs. Juliana, Mr. Ikuemen A john, Mrs. Precious, Ms. Ruth, Mr.
Sako Daga Maryam’s Delight CEO
Ina gaida Iyayena(Mummy da Daddy), sai kawena kamarsu Zeeta, Zeenah, Rahi, Fa’iza(Sweet beb), Anisa sahat mai zobe, Hadidi Safaya, Khairiyya James, Mary Michael, sai Students dina kamar su Safina, Zahratee, Jamlat, Ummitah, Lulu, Safnah, Safiyya Kamlat, Tamallah Irfan, Shamsiyya Mustapha, Nafisa Idris IBB, Salma Aliyu Shahutu, da fatan sun yi sallah da juma’a lafiyya, Amin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kamaru: Jam’iyyun adawa sun ayyana Bakary a matsayin wanda ya lashe zaɓe
Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye.
Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama.
Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma.
“Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a birnin Douala.
Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph“’Yan Kamaru sun yanke shawara. Sakamakon da muke karɓowa daga sassan ƙasar da ma ƙetare ya nuna a sarari cewa, ɗan takarar talakawa, Issa Tchiroma Bakary, ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Oktoba 2025,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta zargi jam’iyyar mai mulki ta CPDM da ƙoƙarin amfani da “tsohuwar hanyar maguɗi,” amma ta ce duk da haka Bakary ya yi mata “mummunar kaye mara misaltuwa,”
Union for Change 2025 ta kuma roƙi hukumomin gwamnati da jami’an tsaro da su mutunta zabin al’umma da zaman lafiya, tare da kira ga ’yan ƙasa da su ci gaba da kasancewa cikin shiri domin kare zaɓinsu.”
Bakary, wanda tsohon minista ne a gwamnatin shugaba Paul Biya, an zaɓe shi a watan Satumba a matsayin “ɗan takarar haɗin kai na jama’a.”
Ƙungiyar, wadda rahotanni ke cewa ta ƙunshi fiye da ƙungiyoyi 50 na siyasa da na fararen hula, ta ce manufarta ita ce haɗa ɓangarorin adawa domin yin aiki tare wajen sauyin siyasa da sake gina ƙasa.
“Ƙungiyar Talakawa ce, wadda take buɗe ƙoa ga kowa — ɗan ƙasa ko ƙungiya, ciki har da waɗanda ’yan takararsu aka hana shiga zaɓen shugaban ƙasa ba bisa ƙa’ida ba,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta bayyana kanta a matsayin sabuwar ƙarfi na farfaɗo da dimokuraɗiyya, tana mai alƙawarin sake gina Kamaru a cikin lokacin canji na shekaru uku zuwa biyar.
A lokacin da ake rubuta wannan rahoto, Hukumar Ƙoli ta Ƙasar ba ta fitar da sakamakon hukuma ba, lamarin da ake ganin zai iya ƙara ɗaga zullumin siyasa a kwanaki masu zuwa.