‘Yansanda Sun Damke Mutum Shida Kan Kisan Da Aka Yi A Kasuwar Abuja
Published: 12th, July 2025 GMT
“Bayan ’yansanda sun yi gaggawar shiga yankin domin kwantar da hankulan jama’a tare da dawo da zaman lafiya, a halin yanzu akwai mutane shida da ake zargi suna tsare a kan lamarin.”
Ya kara da cewa, ‘yansandan sun hada kan shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya wajen tattaunawa, wanda hakan ya taimaka wajen kwantar da hankula.
“Bayan faruwar lamarin, sai muka gana da shugaban al’umma a wurin, sarkin gargajiya yana tare da mu, muka tattauna kuma muka yi kokarin gano abin da ya faru, suka tabbatar mana da cewa za a wanzar da zaman lafiya,” in ji shi.
Ya ce har zuwa ranar Alhamis, Kasuwar Gosa ta koma ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tsauraran matakan sa ido kan ‘yan sanda.
Ajao ya kara da cewa, a kokarin da ake na magance matsalar fashi da makami, wasu laifuka biyar na fashi da makami sun kai ga kama wasu mutane 17, yayin da aka kama wasu 6 da ake zargi da hannu a fashin da aka dakile a Apo da Kubwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yansanda
এছাড়াও পড়ুন:
An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa unguwar Qua da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato.
’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawaAdadin waɗanda aka kashe mutum 32 da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara suna cikin wata mota ƙirar bas mai kujeru 18 daga unguwar Basawa da ke Ƙaramar hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna, domin halartar bikin aure a lokacin da suka haɗu da maharan.
Da yake gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban babbar kotun jihar, lauya mai shigar da ƙara, S.I. Ikutanwa, ya nemi izinin kotun domin waɗanda ake zargin su ɗaukaka ƙara kan tuhume-tuhume huɗu da ake yi musu.
Sai dai lauyan da ke kare waɗanda ake zargin Garba Pwol, ya ƙi amincewa da buƙatar ƙarar, inda ya ce biyu daga cikin mutum 22 ƙananan yara ne, wanda hakan ya sa tuhume-tuhumen ba su da tushe.
A cewar lauyan da ke kare waɗanda ake zargin ’yan shekaru 13 ne da kuma 17, kuma doka ba ta yarda a gabatar ƙananan yara a irin wannan shari’ar ba. Lauyan da ke kare waɗanda ake ƙara ya buƙaci kotun da ta ba shi lokaci domin shigar da ƙara.
Da yake mayar da martani ga lauyan waɗanda ake tuhuma, lauyan mai shigar da ƙara ya ce, tun da biyu daga cikin waɗanda ake zargin ’yan ƙasa da shekaru 18 ne a cire sunayensu, sannan a bar sauran mutum 20 da ake tuhuma su amsa tuhumar.
Da yake tsokaci kan sharia’ar ga ɓangarorin biyu da suka gabatar, alƙalin kotun, Mai shari’a Boniface Ngyon, ya ce zai fi kyau kada a shigar da ƙarar nasu ranar Alhamis, maimakon haka za a yi gyara a ranar Juma’a, ban da ƙananan yara.