Somaliya: Kungiyar Al-Shabab Ta Kai Wa Barikin Soja Hari A Birnin Magadishu
Published: 10th, July 2025 GMT
Kungiyar al-shabab mai alaka da alka’ida ta kai harin kunar bakin wake a wani barikin soja da yake birnin Magadishu a jiya Laraba da marece.
Shaidun ganin ido sun ce, harin ya yi kara mai tsanani wacce ta girgiza babban birnin kasar Magadishu, sannan kuma harbe-harbe su ka biyo baya.
Kungiyar al-shabab mai alaka da alka’ida ce ta dauki alhakin kai harin.
Sai dai kuma babu wani cikakken bayani akan ko harin ya yi sanadin jikkata ko rasa rayuka.
Ita dai kungiyar al-shabab ta dade tana kai hare-hare a cikin kasar Somalia da hakan ya sa gwamnatin kasar take daukar ta a matsayin kungiyar ta’addanci.
A shekarar 2023 ma dai kungiyar ta al-shabab ta kai wani harin kunar bakin wake a cikin barinin sojan, wanda ya yi sanadiyyar kashe sojoji 25. A cikin watan Mayu na wannan shekarar kuwa, an kai wani harin wanda yayi sanadiyyar kashe mutane 10.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross
Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce akwai yara akalla miliyan biyar da dubu 400 da ke fama da matsalar karancin abinci a jihohi tara na arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.
A cewar kungiyar, jihohin su ne Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, Zamfara, Neja, Binuwai da kuma Kano.
Mai rikon mukamin Darktan Lafiya da Kula na kungiyar Dr Aminu Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a yayin taron gangamin neman tallafi kan karancin abinci na kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma da ya gudanar a Kano ranar Talata.
Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a AbujaYa ce daga cikin adadin, akalla yara miliyan daya da dubu 900 ne kuma ke fama da matsanancin karancin abincin, yana mai bayanin cewa akwai alaka mai karfi tsakanin rashin tsaro da karancin abinci.
Dr Aminu ya ce, “Munahimci cewa yaduwar cutar yunwa da sauran cututtuka kamar su maleriya da amai da gudawa da kuma kalubalen tsaro a wasu sassa na Najeriya, ya zama wajibi a dauki matakan kariya da kuma wayar da kan jama’a ta hanyar hada kai da mutane domin lalubo bakinn zaren.
“Duk inda ake da matsalar tsaro, mutane kan kyale gonakinsu su bar yankunan. Sannan mutane da dama sun rabu da muhallansu sun koma ’yan gudun hijira a wasu wuraren. To duk lokacin da aka raba ka da hanyar samun abinci, akwai barazanar fuskantar matsalar yunwa.
“Sannan ba wai iya maganar abinci kawai ake ba, magana ce ta abinci main gina jiki da kuma ruwan sha mai tsafta,” in ji shi.
Shi ma shugaban kungiyar na Najeriya, Prince Oluyemisi Adetayo Adeaga, ya ce karancin abinci babbar cuta ce da ke bukatar agajin gaggawa saboda kada ta ta’azzara.
“Idan ka je asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu, za ka ga yadda jama’a ke tururuwar zuwa saboda cututtukan da ke da alaka da yunwa. Hakan na da barazana ga dan Adam da ci gaban kasa,” in ji shugaban.
Shi ma shugaban kungiya a Kano, Barista Salisu Sallama, ya ce kodayake jihar ba ta da yawan masu fama da cutar idan aka kwatanta da takwarorinta, amma akwai barazana idan aka yi la’akari da halin da ake ciki da zai iya ta’azzara matsalar.