Sojoji sun kama mai garkuwa da mutane da bindigogi
Published: 12th, July 2025 GMT
Sojojin Operation SAFE HAVEN da ke aiki a Arewacin Najeriya, sun kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane a kan hanyar Wamba zuwa Jos, tare da kuɗi Naira miliyan 13 da kuma makamai
Wannan kamen ya faru ne a ranar Laraba, 9 ga watan Yuli 2025, a wani shingen bincike da sojoji suka kafa a Agameti, a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.
A cewar mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, sojojin sun dakatar da wata mota ƙirar Volkswagen mai lamba JJN 336 YZ, ɗauke da mutane uku.
Amma biyu daga cikin su sun tsere kafin a fara bincike.
Bayan duba motar, sojojin sun gano bindigogi biyu ƙirar AK-47, harsashi da yawa, da kuma jini a cikin motar.
Wanda aka kama ya yi ƙoƙarin bai wa sojoji cin hancin kuɗi domin su sake shi, amma suka ƙi amincewa.
Sojojin na ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda suka tsere domin tabbatar da doka da oda a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Mai Garkuwa Da Mutane
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa
Wani mummunan rikicin ƙabilanci a ƙaramar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa ya yi ajalin mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka.
Kakakin ’yan sanda ta jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Salama sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya tare da cafke wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin.
Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai farmaki ƙauyen Dagaceri, inda suka ƙona gidaje tare da kai wa mazauna garin hari da kibau a lokacin da suke barci. Rahotanni sun ce gidaje da dama sun ƙone a harin da ya faru a tsakar dare.
DSP Shiisu ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun ƙwato wayoyin hannu da layu daga hannun waɗanda ake zargi.
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno Soja ya harbe matarsa, ya kashe kansa a Jihar NejaWannan lamari dai ya ƙara haifar da damuwa kan yadda rikicin ƙabilanci ke sake bayyana a wasu sassan jihar Jigawa.
A watan Satumbar 2024, akalla mutane 15 ne aka kashe a wani rikici makamancin wannan tsakanin kungiyoyin Fulani a ƙauyukan Zangon Maje da Yankunama a ƙaramar hukumar Jahun.
Sai dai duk da waɗannan matsalolin, Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewacin Najeriya.
Wani bincike mai zaman kansa da gwamnatin jihar ta gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa Jigawa na cikin jihohi biyar mafi kwanciyar hankali ta fuskar tsaro a cikin gida.
A watan Yuli 2025 Gwamna Umar Namadi ya gudanar da bikin maido da zaman lafiya a ƙaramar hukumar Guri, bayan shekaru da dama na rikicin manoma da makiyaya.
Yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin harin, mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta ƙara tsaurara matakan tsaro da kuma samar da tsarin gargadin gaggawa na al’umma domin hana ci gaba da zubar da jini.