FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”
Published: 11th, July 2025 GMT
An kaddamar da shirin koyar da Sinanci mai taken “Hello China”, na gidan rediyon Nijeriya (FRCN), a Abuja babban birnin kasar. Kusan mutane 100, ciki har da jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai da darakta janar na FRCN Mohammed Bulama ne suka halarci bikin kaddamarwar da ya gudana a jiya Alhamis.
Cikin jawabin da ya gabatar, Yu Dunhai ya ce kaddamar da shirin na koyar da Sinanci da gidan rediyon ya yi, zai samar wa ‘yan Nijeriya wani sabon dandali na koyon harshen Sinanci da fahimtar kasar Sin, tare da samar da kuzari mai dorewa ga hadin gwiwar moriyar juna a fannonin cinikayya da tattalin arzikin tsakanin Sin da Nijeriya
Daga ranar 16 ga wata ne za a fara watsa shirin na “Hello China” a fadin kasar, a kowacce ranar Laraba daga karfe 5 zuwa 5:30 na yamma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
ACReSAL Ta Kaddamar da Kamfen Kula Da Sauyin Yanayi A Makarantu
Kungiyar Kano Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (Kano-ACReSAL) ta kaddamar da yakin neman ilimin sauyin yanayi zuwa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ’Yan Mata da ke Kano a wani bangare na shirinta na “Catch Them Young”. Wato Ilmantar da Matasa.
Gangamin wayar da kan jama’a wani bangare ne na kashi na biyu na yunkurin aikin na jawo dalibai, malamai, da kwararrun muhalli wajen tattaunawa kan sauyin yanayi da kuma shigar da matasa wajen magance shi.
Mukaddashin mai kula da ayyukan, Dr. Abdulhamid Bala, ya sanar da daliban cewa sauyin yanayi ya kasance babban kalubalen da ba za a yi watsi da shi ba.
“Sauyin yanayi ya kasance barazana mai dorewa ga dorewar duniya. Amsarmu dole ne ta kasance cikin dabaru da gaggawa.”
Ya bayyana shawarar mayar da hankali kan yaran makaranta. “Muna jan hankalin matasa ta hanyar shirinmu na ‘Catch Them Young’ saboda su ne wakilan canji. Dole ne mu sanya musu kyawawan halaye na muhalli,”
Dakta Bala ya kuma bukaci dalibai da su taka rawar gani wajen wayar da kan jama’a da tallafawa kokarin kare muhalli.
Masana daga Jami’ar Bayero Kano da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST) Wudil ne suka jagoranci zaman a lokacin wannan horon nan.
Khadija Aliyu/ Kano