2025-07-09@18:40:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14

«tsayar da ɗan»:

    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci Majalisar Dattawa da ta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya. A watan Maris, Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida, bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio. Kotu ta ci tarar Natasha N5m saboda kin bin umarninta ’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike Taƙaddamar ta samo asali ne kan yadda aka canja tsarin zama a zauren majalisar. Bayan dakatarwar, Natasha ta zargi Akpabio da yunƙurin cin zarafinta, inda ta kai ƙara Majalisar Ɗinkin Duniya kan lamarin. A ranar Juma’a, Mai shari’a Binta Nyako ta yanke hukunci cewa dakatarwar watanni shida da aka yi wa Natasha...
    Haka shi ma, shugaban ADC, Cif Ralph Okey Nwosu, ya karyata amincewa da ADA, yana mai cewa batun zama jam’iyya kawance lokaci ya riga ya shude. Ya ce sake bijiro da kawance a hukumance ya faru ne wannan makon, bisa ga shawarar daga dukkan masu ruwa da tsaki. A cewar wani rahoto, NNCG ta yi rajistar ADA a hukumance ga INEC. Wasikar neman rajistar ADA daga INEC an sanya hannu a kai daga shugaban kungiyar na wucin gadi, Cif Akin A. Rickets, da sakataren kungiyar na wucin gadi, Abdullahi Elayo. Hadakar ta kuma gabatar da takardu masu muhimmanci, daga cikin su akwai kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka bayar da manufifinra da tambari da kuma bayanan taron kafa ta. Wasikar...
    Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya ce rahotannin da ya samu na nuna babu gaskiya a labarin da ake yaɗawa cewa mai ƙunar baƙin wake ne ya tada abu mai fashewa a barikin soji na Mogadishu da ke Abuja. Wike ya bayyana hakan ne ga manema labarai, lokacin da ya kai ziyarar duba aikin titunan da za a ƙaddamar domin bikin cikar shugaba Tinubu biyu a kan karagar mulki. Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Borno Bashin da ake bin Najeriya zai koma tiriliyan 162 Ministan ya kuma ja hankalin ’yan jarida kan yaɗa labaran da ka iya jefa firgici a zuƙatan al’umma. Aminiya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a shingen bincike na barikin sojin Mogadishu, kuma...
    Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya shafe sama da shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi. Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar Ogun. A furucinsa da ya amsa laifin, wanda ake zargin ya amince da sayar da sassan jikin mutum ga masu buƙata don samun kuɗin shiga. “Na dogara ne da sayar da sassan jikin mutum tsawon shekaru 10 da suka gabata. Yawancin sassan da nake sayarwa ina tono su ne daga sabbin kaburbura a makabartu, yayin da wasu kuma nake samun su daga gawarwakin da aka...
    Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023. A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi. “Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa. Ɗan Atiku Abubakar ya yi...
    Wata budurwa ’yar kasar China ta janyo muhawara a shafukan sada zumunta bayan ta nuna masaukinta da ba a saba gani ba — banɗaki mai faɗin ƙafa 6 a wurin aikinta, wanda ta biya kuɗin China Yuan 50 kacal, kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533. Kowa yana ƙoƙari ya tara kudi, amma mutum nawa ne za su yarda su kwana a banɗaki don tara kuɗi? HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS Wannan budurwa ’yar garin Hunan a ƙasar China, ta girgiza duniya kwanan nan, bayan ta wallafa hotunan wajen zamanta da ba a saba gani ba – wani ƙaramin banɗaki da ba a amfani da shi...
    Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da ɗanyen mai da man da aka tace farashin Naira, maimakon amfani da dalar Amurka. Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida, rage matsin lamba kan kasuwar musayar kuɗi, da kuma bunƙasa makamashi. ’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Ma’aikatar Kuɗi ta bayyana hakan ne a shafinta na X, inda ta ce wannan ba mataki ne na wucin-gadi ba, sai dai tsari ne da ake son ya ɗore wanda Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, ta aminta da shi. “Wannan manufa za ta taimaka wajen bunƙasa tace mai a gida, rage...
    Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya. Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna. Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD Abubakar ya ce baya ga horaswar, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu. Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...
    Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Mayu. A wata shari’a daban, kotun ta kuma bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, tsohon Manajan Darakta na Kamfanin Zuba Jari da Kadarorin Kano (KSIP), bisa zargin ɓatan Naira miliyan 212.4. A gefe guda ta sake ɗage zaman wannan shari’a saboda abokin shari’ar tasa, Dauda Sheshe, har yanzu bai karɓi sammaci ba. An ɗage shari’arsu zuwa ranar 29 ga watan Afrilu. Dukkanin waɗannan shari’u na da alaƙa da zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a yayin da suke rike da muƙaman gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris. Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira. An hana tashe bana a Kano — Nalako NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Sanarwar ta NNPC na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun ce kamfanin ya dakatar da sayar wa matatar mai a farashin naira, kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya tun da farko. Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Litinin ta ce ba...
    Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016. Ana...
    Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...
۱