Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukumar Hisba Ta Jihar Jigawa
Published: 23rd, July 2025 GMT
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa.
Sanarwar ta bayyana cewa bikin sanya hannun ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnati dake Dutse, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta, ciki har da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon.
Ta ce Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, bayan kai-komo na sama da watanni takwas da bangaren majalisar dokoki da majalisar zartarwa suka yi domin kaiwa ga gaci.
“Yau mun kammala aikin da muka fara kusan watanni bakwai zuwa takwas da suka gabata. Da ikon Allah, an kammala kudurin da ya kafa hukumar Hisba a matsayin cikkakiyar hukuma a Jihar Jigawa,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya yi wa hukumar fatan alkhairi, tare da fatan za ta kawo ƙarin daidaito da tarbiyya a cikin al’umma.
Ya kuma shawarci ma’aikatan Hisba da su kasance masu tsoron Allah, adalci da kuma jajircewa a yayin gudanar da aikinsu.
Gwamna Namadi ya yaba wa kwamitin da ya shirya kudurin bisa himma da sadaukarwa wajen kammala wannan aiki mai muhimmanci.
Bayan sanya hannu kan wannan doka, yanzu hukumar Hisba ta samu cikakken iko na gudanar da aikinta a duk fadin Jihar Jigawa bisa tsarin da aka shimfiɗa na inganta tarbiyya, adalci da walwalar al’umma.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hukumar Hisbah Jigawa Jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, tare da wasu mutane goma sha biyu na samun kulawa a asibiti bayan tsira daga wani hadarin mota da ya faru a kan hanyar Katsina zuwa Daura, a Jihar Katsina.
Hatsarin ya faru ne sakamakon taho-mu-gama da wata motar haya kirar Volkswagen a kusa da Tashar Motoci ta KTSTA da ke Daura.
Duk da cewa hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ba ta fitar da sanarwar hukumance dangane da lamarin ba, shaidu da hotunan da aka dauka daga wurin sun tabbatar da cewa motocin biyu sun lalace matuka.
Shaidun gani da ido sun shaida wa Radio Nigeria cewa motar gwamnan ba ta cikin sahun motocin rakiyar gwamnati a lokacin da hadarin ya faru.
Daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen daukar wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Tarayya na Daura, ya shaida wa Radiyon Najeriya cewa dukkan fasinjoji tara da ke cikin motar hayar sun samu raunuka.
“Mun kai su Asibitin Gwamnati na Daura inda ake kula da su yanzu,” in ji shi.
A halin yanzu, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Katsina, Alhaji Bala Salisu Zango, ya ziyarci fasinjojin motar hayar da suka jikkata a Asibitin Gwamnati na Daura, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin dukkan kudin maganinsu.
Bakwai daga cikinsu sun samu raunuka kadan ne kawai, yayin da biyu kuma suka sami karaya.
“Gwamnatin Jihar Katsina za ta biya dukkan kudin maganinsu kuma za ta ci gaba da kula da lafiyarsu har sai sun warke.” in ji Zango.
Ya kara da cewa gwamnan ma yana cikin koshin lafiya, kuma tuni aka sallame shi daga Asibitin Tarayya na Daura.
“Na yi magana da shi ta waya ba da dadewa ba, yana cikin koshin lafiya. An kwantar da shi tare da sauran wadanda suka jikkata a Asibitin Tarayya na Daura, kuma an sallame shi bayan an tabbatar da cewa lafiyarsa ta daidaita.”
Haka kuma, wata sanarwa da Sakataren Watsa Labarai na Gwamna Radda, Malam Kaula Mohammed ya sanya wa hannu ta tabbatar da cewa gwamnan yana cikin koshin lafiya.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, gwamnan ya bayyana cewa shi da sauran wadanda hatsarin ya rutsa da su suna cigaba da samun kulawa.
Daga Isma’il Adamu.