Natanyahu Ya Amince Da Kissan Masana Fasahar Nukliya Na Kasar Iran
Published: 13th, July 2025 GMT
Benyamin Natanyahu firai ministan HKI ya amince da cewa gwamnatinsa ta kashe masana fasahar Nukliya na kasar Iran da dama, don haka kasar ci gaba a wannan bangaren.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Amurka mai sun a FOX NEWS.
Har’ila yau furucin ya tabbatar da cewa HKI tana zagon kasa wa JMI wacce shirin makamashin nukliyar ta, ta zaman lafiya ce karkashin kula na hukumar IAEA.
Banda haka wannan ya tabbatar da cewa gwamnatin HKI gwamnatin yan ta’adda ce, wacce take kokarin hana zaman lafiya a yankin Asia ta yamma.
Natanyahu ya fadawa FOX NEWS kan cewa, HKI ta sha kishe masana fasahar Nukliya na kasar Iran, amma wadanda ta kashe a yakin kwanaki 12 sun fi sauran daraja a wajensa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA