Tinubu Yana Goyon Bayan Ƙananan Hukumomi Su Ci Gashin Kan Su – Minista
Published: 12th, July 2025 GMT
Ya tunatar da cewa a bara, Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a ya nemi fassarar doka daga Kotun Ƙoli, inda kotun ta tabbatar da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi ’yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi.
“An samu hukunci daga babbar kotun ƙasa da ke nuna cewa kundin tsarin mulkin mu ya tanadi buƙatar ƙananan hukumomi su samu ’yancin kai – su kasance masu cikakken iko da damar aiki a fannoni daban-daban, ko siyasa ko kuma kuɗi,” inji shi.
A cewar sa, bai wa ƙananan hukumomi dama za ta ƙarfafa dimokiraɗiyya a matakin ƙasa da kuma samar da cigaba a cikin al’umma.
Idris ya nuna damuwa kan yadda tsarin ƙananan hukumomi ya raunana a tsawon lokaci, yana nuni da cewa tsarin ya sha bamban da yadda aka tsara shi tun farko.
“Tsawon shekaru, mun shaida yadda ƙarfin ikon ƙananan hukumomi yake ci gaba da raguwa fiye da yadda kundin tsarin mulki ya tanada,” inji shi.
Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda gwani ne wajen kare dimokiraɗiyya, yana da tabbacin cewa ƙarfafa wannan mataki na gwamnati yana da matuƙar muhimmanci domin cigaban dimokiraɗiyya a ƙasar nan.
“Shugaban Ƙasa ɗan dimokiraɗiyya ne na gaske, kuma yana ganin cewa domin dimokiraɗiyyar mu ta kai inda muke fata, dole ne a ƙarfafa wannan mataki na gwamnati,” inji shi.
Ya buƙaci gwamnoni da su mara wa ƙoƙarin Shugaban Ƙasa baya wajen dawo wa da ƙananan hukumomi ƙarfin su yadda masu tsara kundin tsarin mulki suka nufa tun farko.
Ministan ya kuma gode wa tsofaffin kansilolin bisa jajircewar su wajen kare dimokiraɗiyya, tare da roƙon su da su isar da saƙon gwamnatin Tinubu ga jama’ar ƙasa.
“Ina roƙon ku da ku tallafa wa sauye-sauyen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Ba a tsara su domin wahalar da ‘yan Nijeriya ba. E, da farko za su iya kasancewa masu tsauri amma kamar yadda Shugaban Ƙasa ya faɗa, tattalin arzikin mu yana samun daidaito,” inji shi.
Ministan ya bayyana cewa cire tallafin fetur da daidaita farashin musayar kuɗaɗe da aka yi sun haifar da gagarumar riba, wanda hakan ya haifar da ninka kuɗaɗen da ake raba wa jihohi da ƙananan hukumomi domin aiwatar da ayyukan cigaba.
Ya ƙara da cewa kafa kwamitocin cigaba a kowane yanki na ƙasa wani mataki ne na ganin cigaba ya isa kowane lungu da saƙo na Nijeriya.
Tawagar tsofaffin kansilolin ta karrama ministan da Lambar Yabo ta Maida Hankali Kan Jama’a, inda shi kuma ya nuna godiya tare da cewa hakan zai ƙara masa ƙwazo wajen yi wa al’umma hidima.
A nasa jawabin, Sakatare na biyu na ƙungiyar, Mista Cole Michaels, ya yaba da irin yadda ministan yake farfaɗo da hukumomin da ke ƙarƙashin sa domin wayar da kan jama’a kan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu.
Ya ce an bada lambar yabon ne saboda gudunmawar sa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya a ƙasar.
Tawagar ta ƙunshi wakilai daga jihohi daban-daban a ƙasar nan, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar, Mista Auwal Kassim Hassan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Shugaban Ƙasa kundin tsarin
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Bai Taɓa Ba Ni Umarnin Yin Ƙarya Ko Cin Zarafin ’Yan Jarida Ba – Minista
Ya ƙara da cewa, Tinubu na mutunta dimokuraɗiyya da doka.
Haka kuma, gwamnati ta san cewa ba za ta iya aiki yadda ya kamata ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.
Idris ya ce a baya, wasu jami’an gwamnati suna sukar gwamnati, amma shi kullum yana tattaunawa da ƙungiyar ’yan jarida da masu wallafa jaridu domin warware matsaloli cikin lumana.
“Idan muna yin daidai, ku yabe mu,” in ji shi.
“Idan kuma muna kuskure, ku faɗa mana cikin lumana domin mu inganta ayyukanmu.”
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawar mu’amala da kafafen labarai kuma hakan zai ci gaba.
Ya roƙi ’yan jarida ka da su ɗauki wasu ƙananan matsaloli su yi wa gwamnati hukunci a kai gaba ɗaya.
Ya kuma bayyana wani babban ci gaba da aka samu a Nijeriya na dab da samuwa domin za a karɓi baƙuncin Cibiyar Wayar da Kan Jama’a kan Hanyoyin Yaɗa Labarai (MIL) a Jami’ar Open University da haɗin gwiwar UNESCO.
Wannan cibiyar za ta taimaka wajen ilimantar da mutane kan labaran ƙarya da yaɗa jita-jita.
“Da zarar an amince, mutane daga sassa daban-daban na duniya za su riƙa zuwa Nijeriya domin koyon dabarun kafafen yaɗa labarai,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp