Manoma a Jihar Kaduna sun bayyana gamsuwarsu da yadda iri na TELA Hybrid Maize daga kamfanin EcoBasic Seeds ke samar da amfanin gona ba tare da amfani da maganin kwari ba.

 

Sun bayyana hakan ne a Jaji, Jihar Kaduna, lokacin da ‘yan jarida suka kai ziyara gonakin gwaji da kamfanin EcoBasic Seeds ya kafa.

 

Wani daga cikin manoman, Mallam Sabitu Abdullahi, ya bayyana Irin Masara na TELA Hybrid a matsayin masara mai ban mamaki, yana cewa tana bada amfanin gona mai yawa da kuma girbi cikin kwanaki 70 kacal.

 

“Idan duka manoman Najeriya suka rungumi wannan iri, zai taimaka wajen tabbatar da wadatar abinci a kasa,” inji shi.

 

Ya ce ya shafe shekaru uku yana amfani da irin Masara TELA a gonakin gwaji, kuma ba su yi nadama ba.

 

“Ina noma don cin abinci ne da siyarwa. Mun yi tuwo da ita kuma lafiyayya ce,” ya kara da cewa.

 

Sabitu ya bayyana cewa ya dasa irin SAMMAZ 75 T a gonarsa, wanda kuma za a iya sake dasa shi. Ya shawarci sauran manoma su rungumi irin Masara na TELA, tare da bukatar su sayi iri tun kafin damina mai zuwa.

 

Ya koka da cewa kafin zuwan irin Masara na TELA, manoma a Najeriya na fama da asarar amfanin gona saboda fari, kwari irinsu stemborer da sauran su, amma yanzu sun fara cin gajiyar karin amfanin da ya kai kashi 30 cikin 100.

 

Haka zalika, matarsa, Aminat Sabitu, wata manomiya, ta ce ta shiga harkar noma tare da mijinta bayan ganin irin yawan amfanin da irin Masara na TELA Maize ke bayarwa.

 

“Tun da muka fara amfani da irin Masara na TELA, muna samun buhuna 22 daga filin da muke samun buhuna 10,” inji ta, tana mai cewa irin na da juriya ga fari kuma yana karɓar taki sosai.

 

Ta bukaci kungiyoyin mata su fito su fara shuka irin Masara na TELA, tana tabbatar musu ba za su yi nadama ba.

 

Isma’il Shaibu, matashi mai shekara 27 da haihuwa, ya bayyana cewa irin Masara na TELA Maize ita ce masarar da ta fi dacewa.

 

“Da can ina samun buhuna 7, amma yanzu ina samun 13 daga fili ɗaya. Ba sai mun feshi da maganin kwari ba, saboda wannan iri yana da juriya,” inji shi.

 

Ya kara da cewa kafin su gwada TELA suna da ra’ayi mara kyau a kanta, amma tun da suka fara amfani da ita, suka cigaba da nomanta.

 

A wani bangare, Saleh Ahmadu da aka hangosu yana shara a gonarsa, ya ce ya shafe fiye da shekaru 20 yana noma amma bai taba ganin irin TELA Maize ba.

 

“Kwari ba su cika cin ganyenta ba, kuma tana bada yawan amfanin gona. Idan wani iri zai baka buhuna 5, wannan zai baka sau biyu daga fili ɗaya,” ya bayyana.

 

Cov: Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Juriyarshi Kwari Masara

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote

Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa.

Ɗangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara ɗaya da fara samar da fetur a matatar, inda ya ce tafiyar ta kasance cike da ƙalubale tun daga farko.

“A gaskiya tafiyar shekara ɗaya da ta wuce ta yi mana matuƙar wuya. Mun zo mu sauya tsarin kasuwancin man ƙasa. Amma wasu na ganin mun raba su da hanayar cin abinci bakinsu,” in ji shi.

’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba

Ya ci gaba da cewa, “Amma abin da muka yi shi ne mun sa Najeriya da nahiyar Afirka gaba ɗaya su yi alfahari.”

Ɗangote ya ce matatar ta riga ta fitar da lita biliyan 1.8 na man fetur zuwa ƙasashen waje cikin watanni uku da suka gabata, sannan tana da isasshen ƙarfi wajen cika buƙatar cikin gida.

Ya ce tun daga fara aikin matatar a watan Satumbar 2024, dogayen layukan man fetur da suka fi shekaru 50 ana fama da su a Najeriya sun zama tarihi.

Ɗangote ya ƙara da cewa farashin fetur ya sauka daga kusan Naira 1,100 zuwa N841 a wasu jihohi, kuma da zarar sabbin motocin gas (CNG) masu dakon mai sun fara aiki a duk faɗin ƙasar, rage farashin zai fi tasiri.

Ya kuma bayyana cewa sabbin motocin CNG 4,000 za su samar da aƙalla ayyukan yi 24,000, ciki har da direbobi, makanikai da sauran ma’aikata.

“Ba mu kore kowa daga aiki ba, sai dai muna ƙara samar da ayyuka,” in ji shi.

Ɗangote ya zargi masu harkar mai da haɗa kai da ’yan kasuwa na cikin gida da na waje da ƙoƙarin hana nasarar matatar.

“Yadda aka hallaka masana’antar yadi, haka suke ƙoƙarin kashe matatar mu,” in ji shi.

A kan zargin cewa bai wadatar da ƙasa da fetur ba, sai ya mayar da martani da cewa: “Idan ba mu da ƙarfin samar da mai, me ya sa muke fitarwa zuwa ƙasashen waje?”

Ya kuma yi ba’a ga Ƙungiyar Ma’aikatan Mai (NUPENG) wadda ta ce rage farashin fetur na matatar Dangote “kyautar Girka ce.” Dangote ya ce: “Ko da kuwa kyautar Girka ce, ai kyauta ce, za ta kuma ci gaba da kasancewa.”

Ya jaddada cewa abin da Najeriya ke buƙata yanzu shi ne kare masana’antunta, domin ci-gaban tattalin arziki da kuma rage dogaro da shigo da kaya daga waje.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki