Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya baki daya.

Guo Jiakun, ya jaddada muhimmancin taron, kasancewar ya zo a gabar da harkokin cudanyar kasa da kasa ke fuskantar yanayi na tangal-tangal, da ma karuwar daukar matakan kashin kai daga bangare guda, da kariyar cinikayya.

Ya ce, hadin gwiwar sassan biyu, ya haifar da manyan nasarori a baya, wanda hakan ya bunkasa ci gaba da daukakarsu, tare da samar da tarin alfanu ga jama’arsu da yawanta ya kai biliyan biyu, kana ya samar da babbar gudummawa ga raya zaman lafiya, da ci gaban duniya baki daya. Kazalika, hadin gwiwar sassan biyu ya zamo misali na hadin gwiwar cimma moriyar juna, a sabon zamani na dunkulewar tattalin arzikin duniya.

Daga nan sai ya bayyana aniyar kasar Sin ta yin aiki tare da EU, wajen cimma nasarar taron, matakin da zai aike da kyakkyawan sako ga duniya, game da aniyarsu ta hada karfi da karfe, wajen kafa hadin gwiwa mai karfin gaske, da daga martabar cudanyar mabambantan sassa, da bude kofa da aiwatar da hadin gwiwa. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza

Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka.

“Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem.

Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen duniya da gaza aiwatar da dokokin kasa da kasa, yana mai cewa, “Shiru da kasashen duniya suka yi, abin Allah wadai ne ga gwamnatocin kasashen duniya, musamman na kasashen musulmi da larabawa.

Da yake ishara da kiraye-kirayen baya-bayan nan da kasashe  sama da ashirin suka yi na a dakatar da yakin, Sheikh Qassem ya yi ishara da cewa irin wadannan kalamai da cewa ba su isa ba ko kadan, Ya ce, “bai isa ba a ce kasashe 25 sun yi kira da a dakatar da yakin Gaza, wannan furucin kadai bai wadatar ba.

Sheikh Qassem ya yi kira da a kakaba takunkumi kan “Isra’ila”,  da gurfanar da su a gaban shari’a, da kuma dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
  • Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
  • Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
  • Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.
  • An kaddamar Da Wani Shiri Na Ba ‘Yan Mata 200,000 Tallafin Audugar Mata A Kano
  • Birgediya Janar Sabahi Fard Ya Jaddada Cewa: Duk Wani Sabon Hari Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Gauni
  • Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco