Uganda Ta Bude Kan Iyakarta Da Bangaren Dake Karkashin M23 A Kasar DRC
Published: 13th, July 2025 GMT
Watanni shida bayan da kasar Uganda ta rufe iyakokinta da DRC, saboda yadda kungiyar M23 take kama yankuna, ta sake bude ta a halin yanzu.
Jami’in sojan kasar Uganda, Chris Magezi ya tabbatar da sake bude kan iyakar a wata sanarwa da ya yi ta kafar sadarwa ta al’umma, yana mai cewa an yi hakan ne bisa umarnin shugaban kasar Yoweri Museveni.
Har ila yau jami’in sojan kasar ta Uganda ya ce za a gudanar da bincike akan wadanda su ka jawo rufe iyakar da ya kawo tsaiko a harkokin kasuwanci a tsakanin al’ummun kasashen biyu.
Wannan matakin da gwamnatin kasar ta Uganda ya biyo bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya ce a Washington, inda Rwanda da DRC su ka amince da taimakawa tattaunawar da za a bude a nan gaba a tsakanin kungiyar ta M23 da kuma sojojin gwamnatin kasar ta DRC.
Ita dai kungiyar M23 ta ‘yan kabilar Tutsi ce, wacce tun a 2021 tawayenta ya sake kamari. A wannan shekarar ta 2025 da ake ciki, fada ya yi tsanani da ya kai ga kungiyar ta kama yankuna masu girma a gabashin DRC da su ka hada da Goma da Kivu.
Gwamnatin kasar DRC, tana zargin kasar Rwanda da taimakawa ‘yan tawayen na kungiyar M23 da makamai da kuma sojoji. Ita ma kasar Amurka ta tabbatar da wannan zargin ta hanyar gabatar da dalilai na sirri da ta tattara.
Ita dai kasar ta Rwanda ta sha karyata cewa tana da hannun a tawayen kungiyar M23.
Gabashin kasar ta DRC dai yana da ma’adanai masu kima da ake nema ruwa jallo a duniya domin yin kere-kere na zamani.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kungiyar M23
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA