Aminiya:
2025-07-23@05:08:03 GMT

An rufe masana’antu 1,724 bisa rashin bin dokokin aiki a Guinea

Published: 22nd, July 2025 GMT

Gwamnatin ƙasar Guinea ta rufe wasu sassan kamfanoni guda 1,724 sakamakon kama su da laifin ƙin bin dokokin hukuma, yayin da aka janye kayayyakin da suke sarrafawa daga kasuwa.

Sanarwar na zuwa ne ƙarƙashin ma’aikatar kasuwanci a ƙasar, tana mai cewa an ɗauki matakin ne don kare lafiyar masu sayen kayayyakin da kuma tabbatar da kare muhalli, da kuma tilasta musu biyayya ga dokokin tafiyar da kamfanoni.

Ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar ta ce ba shakka wannan mataki zai zama tamkar hannunka mai sanda ga sauran kamfanoni da ke tafiyar da ayyukansu ba dai-dai ba.

Da yake magana shugaban ƙungiyar masu sayen kayayyaki na ƙasar, Ousmane Keita, ya ce tun shekaru sama da uku suke ta wannan kiraye-kiraye, amma ba a sami damar daukar mataki ba sai yanzu.

NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa An wajabta wa ɗaliban firamare mallakar lambar NIN a Bauchi

A cewar sa ba shakka wannan matakin zai sassauta yadda kamfanonin ke wasa da aikinsu da kuma jefa rayukan jama’a cikin hadari.

Bayanai sun ce a yanzu gwamnati zata mayar da hankali wajen sayawa kamfanonin da ke sarrafa ruwan sha idanun ganin muhimmancinsa ga lafiyar dan Adam.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kayayyaki

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido Kirikasamma

Kwamatin kananan hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya duba ayyukan raya kasa da karamar hukumar Kirikasamma ta samu nasarar gudanarwa daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu.

Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya kafa kananan kwamitoci guda biyu domin samun nasarar tantance ayyukan a cikin garin   Kirikasamma da kauyuka.

Karamin Kwamati na daya bisa jagorancin wakilin mazabar
Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashimu Kanya, ya duba aikin sanya soma da tona riniyar tuka tuka a mayanka da magudanin ruwa a garin Marma da aikin gina rumfunan kasuwa a garuruwan Tasheguwa, Marma, Dilmari da Madaci.

Alhaji Ibrahim Hashim Kanya ya bayyana wa shugaban kamsilolin karamar hukumar wanda ke yiwa tawagar rakiya, Malam Isyaku Abdullahi, muhimmancin ziyarar duba ayyukan Gwamnati dan tabbatar da inganci.

Sai Kuma karamin Kwamati na biyu bisa jagorancin wakilin mazabar Kiyawa Alhaji Yahaya Muhammad Andaza wanda ya duba aikin gyaran hanyar Gafta zuwa Baturiya akan fiye da naira milyan 4 da dubu dari 2, wadda ambaliyar ruwa ta lalata a daminar bara da kuma aikin gina rumfar kasuwa a garin Baturiya.

Tun da farko a sakatariyar karamar hukumar Kirikasamma, Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa Kuma wakilin mazabar Gwiwa,
Alhaji Aminu Zakari ya ce ziyarar Kwamatin na daga nauyin da tsarin mulki ya dorawa bangaren majalisa wajen duba manufofi da shiryeyen Gwamnati baya da yin doka da amincewa da kasafin kudin kowacce shekara.

Alhaji Aminu Zakari ya ce Kwamatin Yana duba kundin bayanan harkokin Kudi da na sha’anin Mulki da su ka hadar da littafin shiga da fitar kudade da takardun biyan kudade na voucher da alkaluman tattara kudaden shiga da kundin tarukan kwamitocin karamar hukuma domin tabbatar da kashe kudaden Gwamnati ta hanyar da ta dace domin wanzuwar shugabanci nagari.

A cewar sa, daga yanzu Daraktan tsare-tsare ya zamo daga cikin masu rattaba hannu kan takardun kashe kudade, mataimakin shugaban karamar hukumar zai rike sashen kula da ruwa da tsafta a matsayin Kansila maras gafaka.

Yayi nuni da cewar, akwai bukatar karamar hukumar ta gina ajujuwa guda 2 na makarantun ‘ya’Yan fulani makiyaya domin shigo da su cikin tsare tsaren ci gaban al’umma.

A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Kirikasamma, Alhaji Muhammad Maji Wakili Marma, ya lura da gudummawar da bangaren majalisa ke bayarwa wajen gudanar da harkokin Gwamnati a matakin jiha da kananan hukumomi.

Alhaji Maji Wakili ya bada tabbacin aiki da shawarwari Kwamatin domin karfafa matarka cigaban karamar hukumar.

Sauran Yan Kwamatin sun hadar da mataimakin shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama Alhaji Sani Sale Zaburan da sakataren Kwamatin Kuma Akawun Majalisa Alhaji Yusha’u Muhammad, da oditoci biyu da mataimakan sakatare.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido Kirikasamma
  •  Kungiyar Malaman Musulmi Ta Yi Fatawar Wajabcin Kawo Karshen Killace Gaza
  • Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21
  • NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa
  • Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC
  • Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – Natasha 
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Shirin Ba Da Horo A Kasar Sin Ya Taimaka Wa Inganta Masana’antar Gyadar Senegal
  • Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar