Aminu Ado ya soke hawan salla don gudun rikici a Kano
Published: 27th, March 2025 GMT
Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na gudanar da bikin hawan salla bayan shawarwari da dattawa da malaman addini suka ba shi.
Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatar tabbatar da zaman lafiya a jihar, biyo bayan shiga ruɗani da jama’a suka yi.
Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga ruɗani a Kano saboda rikicin masarauta, biyo bayan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Tun farko, duka sarakunan biyu – Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin al’umma.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, Sarki Aminu, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan jin ra’ayin malamai da dattawa.
“Malamai da dattawa sun shawarce mu, kuma muna mutunta su. Don haka, bayan nazari tare da majalisar masarauta, mun yanke shawarar cewa mun janye domin zaman lafiya,” in ji shi.
Idan za a tuna, a makon da ya gabata ne, Aminu Ado, ya aike wa ’yan sanda takardar neman izinin gudanar da hawan salla, bayan da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci Muhammadu Sanusi II, ya shirya yin hawan salla a bana.
Sarkin ya jaddada cewa bikin hawan salla ba abu ne da ya zama wajibi ba idan zai iya haddasa rikici da asarar rayuka.
“Idan akwai fargabar cewa hawan salla zai haddasa tashin hankali da asarar rayuka ko dukiyoyi, to, yana da kyau a daina,” in ji shi.
A gefe guda, al’ummar Kano sun nuna damuwa kan yadda rikicin masarautar ke ci gaba da yin tasiri a rayuwarsu.
Ana sa ran wannan matakin zai rage fargabar da ake ciki, tare da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminu Ado Bayero Fargaba gwamna hawan salla Rikicin Masarauta Ruɗani Soke Hawan Salla hawan salla
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa.
M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.
Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade ana yi, don haka a shirye muke mu gudanar da zagaye na gaba na shawarwari da su a birnin Rome.
Babban jami’in diflomasiyyar ya kara da cewa, Tehran na da burin warware batun nukiliyarta cikin lumana.”
Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki na baya-bayan nan na kudaden da Iran ta toshe saboda takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata, Araghchi ya ce daskararrun kudaden na daga cikin takunkumin da ya zama dole a dagewa iran.
Kawo yanzu Iran da Amurka sun yi tattaunawa har uku ta farko a Oman, ta biyu a Italiya sai kuma wace aka gudanar a ranar Asabar data gabata a Oman.
Dukkanin bangarorin na cewa akwai fata mai kyau a jerin tattaunawar da suka gabata.