“A wajen jahilai, tsagaggen lebe lahani ne a kan makogwaro da lebe, amma idan akwai shinge tsakanin hanci da baki, ana kiran sa da suna handa. Wani abu ne da ba a san abin da yake kawo shi ba, amma kuma ana danganta shi da abubuwa da dama kamar karancin rashin sinadarin bitamin B.”

“Don haka, muna shawartar mata masu juna biyu da su mayar da hankali wajen yawan zuwa awon ciki, sannan kuma su rika shan magungunan da ake ba su na yau da kullum, ta yadda za a rage haihuwar masu dauke da wannan cuta.

“Hakika wannan babban abin takaici ne a cikin al’umma, shi yasa kwararrun likitoci, ma’aikatan jinya, jami’an jin dadin al’umma da likitocin makogwaro, hanci da kunne suka taru, domin ganin abin da za mu iya yi da zai kawo wa al’umma sauki tare da karfin tattalin arziki a tsakaninsu a wannan kasa”, in ji shi.

Har ila yau, da yake zantawa da manema labarai, Daraktan kula da lafiya na asibitin kashi na kasa da ke Jihar Inugu, Farfesa Emmanuel Iyidiobi ya bayyana cewa; kulawa da masu matsalar tsagaggen lebe, na daya daga cikin manyan manufofin da wannan asibiti ya sanya a gaba don ganin ya cimma, yana mai jaddada cewa; wani bangare ne na aikin tiyata, ya gara da cewa, wasu daga cikin sassan sun hada da kula da wadanda suka kone, tiyata da dai sauran makamantansu.

“Mun yi hadin gwiwa da kungiyar ‘Smile Train’ fiye da shekara goma da ta wuce, domin kula da marasa lafiya. Kazalika, zan iya fada muku cewa; bayanai sun nuna cewa, mun fi kowane asibiti a Nijeriya yawan yin wa marasa lafiya tiyata”.

“Don haka, ba wani abu ba ne na daban don mun karbi bakuncin wannan taro na bana, sannan kuma mun ji dadin yin hakan kwarai da gaske. Kazalika, me yasa muke yin hakan? Da farko dai, hakan ya yi daidai da muradun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

“Sannan, sabon kudirin nan na shugaban kasar game da kiwon lafiya, ya mayar da hankali tare da karfafa asibitoci wajen inganta harkokinsu ta hanyar horaswa da bincike ta yadda daga wasu kasashen na waje za a rika zuwa a matsayin yawon bude ido tare da neman lafiya a wannan kasa, shi yasa muka yanke shawarar tallafa wa taron ka’in da na’in”, in ji shi.

Har ila yau, a nata jawabin, mataimakiyar shugabar kungiyar ‘Smile Train’, Darakta a shiyyar Afirka, Madam Nkeiruka Obi ta ce; kungiyar ta yi imanin cewa; duk yaron da aka haifa da matsalar datsattsen lebe, ya cancanci samun cikakkiyar kulawa daga kwararru, wadanda suka samu horo a cikin gida Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Jarirai

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

 

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na JKS ya amince da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Sin za ta yi amfani da wannan damar don ci gaba da gyare-gyaren tattalin arzikinta, da kuma fadada bude kasuwancinta mai zurfi ga ketare, ta haka za ta ci gaba da ba da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik da sauran kasashen duniya ta hanyar zamanantar da al’ummarta. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma  October 30, 2025 Daga Birnin Sin Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna
  • Karamar Hukumar Gwarzo Ta Karfafa Yaƙi Da Miyagun Kwayoyi Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba