HausaTv:
2025-07-12@16:07:46 GMT

NYT: Natanyahu Yana Tsawaita Yaki A Gaza Don Ci Gaba Da Kasancewa Kan Iko A HKI

Published: 12th, July 2025 GMT

Jaridar NYT ta kasar Amurka ta bayyana cewa firai ministan HKI Benyamin Natanyaho da gangan yake tsawita yaki a Gaza don tsawaita zamansa a kan kujerar shugabancin kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani binciken da Jaridar New York Times ta yi, inda take cewa Natanyahu ya san cewa matukar ya sauya matsayinsa na shugaban gwamnatin HKI to kuwa sammashin kamasi da kuma tuhume-tuhumen da ake masa zasu tashi wadanda zasu zama masa matsala, kuma a lokacin hatta gwamnatin Amurka ba zata iya yi masa wani taimako ba.

An fara yaki a Gaza ne a ranar 07 ga watan octoban shekara ta 2023 . daga lokacin ya zuwa yanzu sojojin Natanyahu sun kashe falasdinawa kimani 57,000. Sannan an jikata wasu fiye da 12000. Banda haka sun rusa fiye da kasha 90% na gaza. Sannan sun hana shiga abinci da ruwa har ya kaiga falasdinawa da dama sun mmutan saboda yuwan da rashin lafiya da wasu dalilai.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Babban Kwamandan Sojin Iran Ya Bayyana Cewa Iran Ta Koyawa Gwamnatin Isra’ila Hankali

Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran

Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya.

A wata ganawa da iyalan shahidi Kanar Bostan Afrouz, Manjo Janar Hatami ya kara da cewa: Makiya sun kasa cimma tsare-tsare da shirye-shiryensu da suka rigaya sukaaniyar cimmawa, kuma sun fuskanci mummunar martani da shan kashi.

Ya ci gaba da cewa: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya duk da karfin soja da kudi da suke da su, baya ga bayanan sirri da suke tabbatar da samun goyon bayan gwamnatin kama karyar Amurka, wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Tana Nazarin Sakon Amurka Na Bukatar Farfado Da Tattaunawa Shirin Makamashin Nukliya Na kasar
  • Lavrov: Shuwagabannin Kasashen Yammacin Turai Suna Son Shiga Yaki Da Rasha
  •   Fiye Da Falasdinawa 60 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i Kadan
  • Amurka Ta Rage Wa’adin Bizar ‘Yan Nijeriya Zuwa Wata Uku
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Jagora Da Kansa Ya Shiga Dakin Ba Da Umarnin Sojin Lokacin Yaki
  • Babban Kwamandan Sojin Iran Ya Bayyana Cewa Iran Ta Koyawa Gwamnatin Isra’ila Hankali
  • Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza
  • Zagaye na 5 A Tattaunawar Gaza da HKI  Ya tashi ba tare da Sun Dai-daita ba A Doha
  • HKI: Sojoji 62 Ne Su Ka Halaka A Gaza A Cikin Wannan Shekara Ta 2025