HausaTv:
2025-07-11@22:22:39 GMT

Najeriya Ba Za Ta Karbi ‘Yan Ci Ranin Kasar Venezuela Da Amurka Za Ta Kora Ba

Published: 11th, July 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar  wanda ya yi hira a wata tashar talbijin din kasar ya yi amfani da salon maganar wani mawakin Amurka  mai suna Flavour Flav da ya shahara a shekarun baya, wajen mayarwa da shugaban Amurka Donald Trump martani da cewa: Babu abinda zai iya yi ma ka.

Jaridar Wall Street Jouran ta buga labarin dake cewa; A yayin taron da aka yi a tsakanin wasu shugabannin kasashen Afirka biyar da shugaban kasar Amurka a fadar White House, an bijiro musu da karbar bakuncin ‘yan ci-ranin kasashe waje da Amurka take son kora daga cikinta.

Jaridar ta ambaci Nigeria a cikin kasashen da Amurka ta bijirowa da bukatar ta karbi bakuncin ‘yan ci-ranin kasar Venezuela su 300.

Ministan ya bayyana karbar bakuncin ‘yan ci-ranin a matsayin wani Karin nauyi akan kasar wacce take fama da nata yanayin na musamman.

Amurka ta yi barazanar karawa Najeriya kudin Fito na kayan kasuwanci idan ba ta amince ta karbi ‘yan ci-ranin ba, ko kuma a hana ‘yan kasar Visa ta shiga Amurka.

Sai dai ya ce; kasar a shirye take ta yi hulda da Amurka a cikin fagagen ma’adanai, iskar Gas da kasuwanci.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yan ci ranin

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Yace Huldar kasar Iran Da IAEA Zai Ci Gaba Ne Idan Ta Daina Fuska Biyu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya fadawa shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa, kan cewa huldar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA zai kasance tare da sharudda. Saboda hukumar ta yi watsi da ayyukanta na asali ta koma siyasa. Ta fita daga bangaren kwararru ta zama tana bin bukatun wasu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar ta IAEA a da can ta zuciya guda ce, bata boyewa hukumar wani abu a cikin ayyukanta na makamashin Nukliya. Amma a halin yanzu mun gano cewa hukumar ce take bawa HKI bayanai dangane da ayyukammu na Nikliya ta kuma bada sunaye dadireshin masana fasahar Nukliya na kasar HKI ta zo ta kashesu kai tsaye ko kuma ta yi amfani da wakilanta a cikin Iran don yin wannan aikin.

Banda haka Hukumar ta rufe idanunta kan shirin makaman Nukliya na HKI gaba daya.  Daga karshe yace Iran zata sauya yadda take hulda da hukumar a lokaci guda tana bin hanyar diblomasiyya don warware matsalolin da suke rage tsakaninta na hukumar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Iran Yace Huldar kasar Iran Da IAEA Zai Ci Gaba Ne Idan Ta Daina Fuska Biyu
  • Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita
  • Ministan Tsaron Iran Ya Bayyana cewa: Martanin Da Iran Ta Mayar Ne Ya Sanya Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta
  • Manazaecin Kasar Amurka Ya Ce; Isra’ila Ta Sha Kashi A  Yakinta Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Aragchi Ya Tattauna Da Bin Salman Kan Karfafa Zumunci Tsakanin Kasashen Biyu
  • Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza
  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Idan Tanaso
  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliya Kasar Idan Tanaso
  • Iran Ta Tabbatar Da Cewa Tana Iya Yakar Amurka Da HKI A Lokaci Guda