Gwamnatin Jihar Jigawa ta nuna matukar gamsuwa tare da yabawa Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr Builder Muhammad Uba bisa kokarin sa na ayyukan raya kasa.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bude ofishin shugaban karamar hukumar da kuma dakin taro na karamar hukumar da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar ta Birnin Kudu.

Ya ce shugaban karamar hukuma, Dr Builder Muhammad Uba mutum ne mai kwazo da himma wanda ya zamto abin koyi a bangaren shugabanci.

A don haka, Malam Umar Namadi ya yi kira ga sauran shugabanin kananan hukumomin jihar da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukan kyautata rayuwar al’ummar su domin sharbar romon mulkin dimokradiyya.

A jawabinsa na godiya shugaban ƙaramar hukumar, Dr Builder Muhammad Uba ya godewa Gwamnan bisa samun damar bude ofishin da kuma dakin taro na karamar hukumar.

Wakilinmu ya ba mu rahoton cewar, Gwamnan ya sami rakiyar Mataimakinsa, Injiniya Aminu Usman Gumel da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatun da Sakataren Gwamnati Alhaji Bala Ibrahim da Shugaban Jami’yya na Jihar Alhaji Aminu Sani Gumel da Kwamishinoni da sauran mukarraban gwamnatin jihar.

 

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa karamar hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin

Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ta ce ta ceto wani bene mai hawa biyu daga rugujewa gaba daya sakamakon wata gobara da ta tashi a garin Ilorin.

 

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda y ace gobara da ta tashi a hanyar Muritala Muhammed, daura da Cocin C & S, Ilorin.

 

A cewarsa da isar su, ma’aikatan kashe gobara sun gano cewa wani gini mai hawa biyu da ya kunshi dakuna 8 da shaguna 10 na fuskantar barazana. Ya bayyana cewa, ta hanyar daukar mataki cikin gaggawa da hadin kai, jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar yadda ya kamata, tare da hana yaduwarta zuwa gine-ginen da ke kewaye, inda ta kara da cewa a sakamakon haka, daki daya ne lamarin ya shafa.

 

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wutar lantarki ce dalilin ta tashin gobarar.

 

Da yake mayar da martanin Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara Prince Falade Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su kasance cikin shiri da kiyaye lafiya a gidajensu da wuraren kasuwancinsu.

 

REL/ALI MUHAMMAD RABIU

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukumar Hisba Ta Jihar Jigawa
  • Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido Kirikasamma
  • Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
  • Hisbah Ta Lalata Barasa Ta Naira Miliyan 5.8 A Jigawa
  • Wata Kungiyar Ta Bukaci Shugaban Kasa Ya Cika Alkwarin Marigayi Shugaba Buhari Game Da Shehu Usman Aliyu Shagari
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin
  • APC Ta Zabi Kamilu Sa’idu A Matsayin Dan Takarar Kaura Namoda Ta Kudu A Zamfara
  • Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar