Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Ƙarshe Tsakanin Chelsea Da PSG
Published: 13th, July 2025 GMT
3. Girman Lambar Yabo da Za a Baiwa Zakaran Gasar
Kungiyar da ta lashe kofin za ta samu fam miliyan 97 daga hukumar FIFA. Hakanan, za ta sanya tambarin kofin na tsawon shekaru 4, sabanin shekara 1 da ake yi a baya.
4. Muhimmancin Wasan ga Duka Kungiyoyin
Ga PSG, wannan kofi na iya zama jaddawalin nasarar su bayan barin Kylian Mbappé.
5. Kallon Duniya na Kan Wasan
Wasan zai jawo hankalin masu sha’awar kwallon kafa a duniya, musamman ganin yadda kowanne bangare ke dauke da fitattun ‘yan wasa da kocin da ke kokarin kafa tarihi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere.
Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha.
Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru.
Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana cewa: yana da burin samun Ballon d’Or masu yawa idan ya samu dama.
Matasa da dama sun so Yamal ya lashe Ballon d’Or a wannan shekara, musamman irin kokarin da ya yi a bara, da kuma lashe kyautar gwarzon matashin danwasa da ya yi a bara. Kuma rashin samun kyautar ba ta yi wa matasa da dama dadi ba.
Ana ganin samun nasara a tawagar ‘yan wasan kasar Sifaniya zai fi ba shi damar lashe kyautar fiye da kungiyarsa ta Barcelona, amma idan har Barcelona ta iya lashe gasar cin kofin zakarun turai tabbas zai iya lashewa.
Amma kuma akan fifita nasarar da dan wasa ya yi a kasarsa fiye da kungiyar da yake bugawa wasa, kuma a bayyane take Kofin Duniya na daya daga cikin manyan abubuwan da zai sa mutum ya lashe kyautar.
Saboda haka idan har Sifaniya ta lashe kofin duniya a shekara mai zuwa ta 2026, Yamal zai iya samun kyautar Ballon d’Or. Kasancewar a yanzu yadda yake da cikakken gurbi a tawagar kasar, babu yadda za a yi Sifaniya ta ci kofin ba tare da kwallayensa ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA