HausaTv:
2025-07-23@17:54:06 GMT

Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa

Published: 23rd, July 2025 GMT

Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran.

Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan  Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a kasar Iran nan gaba bisa tsarin dokokin kasa da kasa.

Wannan yunkuri yasa an ga bangarorin biyu na Amurka da Isra’ila suna matsa lamba a kan sauran bangarori na duniya, tare da bayyana Shirin na Iran a matsayin mai matukar hadari ga duniya, da nufin samun goyon bayan kasashen duniya kan bakaken manufofisu a kan kasar ta Iran.

Dangane da zargin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan Shirin Iran da kuma neman samoma kansa hujjoji na kaiwa Iran hari, da kuma bayyana cewa harin Amurka ya kawo karshen Shirin Iran na nukiliya, Pezeshkian ya ce, “Da’awar cewa shirinmu na nukiliya ya kawo karshe, batu ne na yaudara.”

“Ilimin nukiliya yana a cikin kwakwalen masananmu ne na kimiyyarmu, ba a cikin wurarenmu ba.” In ji Pezeshkian.

Haka nan kuma shugaban na Iran ya sake nanata matakin kin amincewa da zargin kasarsa da hakoron kera makaman kare dangi, da kuma kara jaddada matsayin kasar na ci gaba da daukar matakan da take yi wajen kara inganta shirinta na makamashin nukiliya domin ayyukan farar hula.

Pezeshkian ya kuma sake nanata shirye-shiryen Iran na yin shawarwarin da ba su ginu a kan haramtawa Iran hakkinta na inganta na tace sanadarin Uranium ba, amma ya ce “duk wata tattaunawa da za a yi a nan gaba dole ne ta dogara a kan batutuwa na masu tabbatar da hakkokin Iran.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Uranium A Cikin Kasarta

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa; Ba zai yiwu Iran ta iya yin watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Har yanzu ba a daina sarrafa sinadarin Uranium ba a Iran, duk da irin barnar da hare-haren Amurka ya yi wa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran.

A wata hirarsa da Fox News, Araqchi ya amsa tambayoyi kan cewa: “Shin shirin inganta sinadarin Uranium a Iran ya dawo? Shin har yanzu yana ci gaba, ko kuma barnar da aka yi wa Iran ya yi tsanani har ta kai ga dakatar da shi gaba daya?” Araqchi ya amsa da cewa; “Ba a daina bainganta sinadarin ba, duk da cewa barnar ta yi tsanani, amma duniya ta sani Iran ba za ta iya yin watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba saboda muhimmancinsa, domin wannan nasara ce ta masana kimiyyar kasar, kuma a halin yanzu abin alfahari ne ga kasa, kuma inganta sinadarin Uranium yana da matukar muhimmanci ga Iran.”

Da yake amsa tambayar cewa: “Mene ne dalilin da ya sa Iran ba za ta shigo da sinadarin uranium da ake inganta shi daga waje ba kamar yadda wasu kasashe ke yi? Araqchi ya ce: “Saboda wannan nasara ce ta ilimi, nasara ce da kasar Iran ta samu, to me ya sa za mu shigo da shi daga waje, duk da za ta iya samar da kanta?”.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Uranium A Cikin Kasarta
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
  • Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
  • Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
  •  Kungiyar Malaman Musulmi Ta Yi Fatawar Wajabcin Kawo Karshen Killace Gaza
  • Fizishkiyan: Batun Kare Hakkin Bil’adama Ba Komai Ba Ne Sai Karya
  • Shirin Ba Da Horo A Kasar Sin Ya Taimaka Wa Inganta Masana’antar Gyadar Senegal
  • Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne
  • Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco