Akwai Bukatar Hada Kai Da Aiki Tare Tsakanin Hukumomin Tsaro
Published: 11th, July 2025 GMT
Hukumomin tsaron uku su ne, na DIA, DSS da kuma NIA, inda kuma dokar, ta bayar da damar kafa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro wato ONSA, wadda a baya, ake kiran ofishin da Babban Jami’in Tsaro na Kasa wato CONS.
Wannan Jaridar, na nuna matukar damauwarta kan ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro, da Nijeriya ke fuskata, musamman na rashin gazawar hukumomin tsaro na sirri saboda gasar da suke nuna wa, a tsakaninsu.
A bisa ra’ayinmu, wannan matsalar, abu ne da ke bukatar a kara mayar da hankali cikin gaggawa domin a magance wannan kalubalen na rashin na rashin tsaron.
Sai dai, muna kuma yabawa kokarin da hukumomin tsaron ke ci gaba da yi, na lalubo da mafita kan kalubalen na rashin tsaro.
Amma abin takaici ne, kan yadda gasar a tsakanin hukumomin tsaron kasar, ke kara haifar da kalubalen na rashin tsaro wanda kamata ya yi ace, suna yin aiki tare, domin a samar wa da ‘yan Nijeriya sauki, wajen magance masu kalubalen rashin tsaron, da suke ci gaba da fuskanta.
Hatta shi ma tsohon Babban Hafsan Tasron kasar ya tabbatar da cewa, akwai bukatar hukumomin tsaro na sirri na kasar, su kara zagaewa wajen samar da dabarun kara ciyar da hukumomin na tsaro.
Wasu kwararru na ganin cewa, akwai bukatar hukumomin tsaron su hada kai domin samar da tsaro a kasar.
Gasar da ke ci gaba da aukuwa a tsakanin hukomomin tsaron su kasance suna samar da bayanan sirri a tsakaninsu, domin a dakile kalubalen rashin tsaro a kasar.
Masu ruwa da tsaki a kasar, ciki har da shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ci gaba da nuna damuwarsu, kan kalubalen rashin tsaro a kasar, musamman duba da yadda Tinubu, a wani taro na kwanan baya ya sanar da cewa, kalubalen rashin tsaro a karni na 21, abu ne da ake bukatar hada kai, amma ba wai batun nuna yin gasa, a tsakanin hukumomin tsaron kasar ba.
Kalubalen ta’addanci a Arewa Maso Gabas, matsalar ayyukan ‘yan bindiga a Arewa Maso Yamma, fashi a Tekunan ruwa a Tekun Guinea, rikicin manoma da makiyaya a yankin Middle-Belt, batun ‘yan aware a yankin Kudu Maso Gabas, wadannan matsalolin, abu ne, da yafi karfin hukumar tsaro daya, ta kawo karshensu.
Kazalika, hare-haren da suka janoyo kashe wasu kauyawa kimanin su 200 a daren ranar 13 na watan Yunin 2025 yankin Yelwata, na karamar hukumar Guma a jihar Biniwe da kuma sake dawor ayyukan ‘yan ta’addar Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas, hakan ya nuna a zahiri, akwai bukatar hukumomin tsaron su hada kai domin tunkarar kalubalen na rashin tsaro da kuma kawo karshen sa, musamman duba da cewa, matsalar na kara zama barazana ga tattalin arzikin.
Sai dai, hakan ya nuna cewa, kusan babu wani katabus da hukumomin tsaron ke yi, na magance kalubalen na rashin tsaron.
A ra’ayin wannan Jaridar, akwai matukar bukatar Gwamnati ta dauki kwararan matakai, musamman domin gano ainahin tushen matsalar ta rashin tsaro, da kuma magance ta.
Sai dai, wani kokari daya shi ne, na kara fadada mahukuntan na tsaron sirri wato kafa cibiyar kasa ta dakile yunkurin ayyukan ta’addanci NCTC.
Bukatar hukumomin tsaron na sirri, na yin aiki a tare, abu ne da yake da matukar mahimmanci, musamman domin a magance kalubalen rashin tsaro, da Nijeriya ke fusanta.
Ra’ayin wannan Jaridar shi ne, akwai bukatar hukumomin tsaro na sirri na kasar, su jingine batun gasa a tsakaninsu, su mayar da hankali, wajen lalubo da mafita, kan kalubalen rashin tsaro a kasar.
Kazalika, duba da irin yanayin na barazar rashin tsaron, ya kamata a kara zuba kudade wajen kara darajar kayan kimiyya na aikin tsaro na hukumomin tsaron kasar, wanda hakan zai kara masu kwarin guiwar, kara mayar da hankali a ayyukansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Nijeriya akwai bukatar hukumomin tsaro kalubalen na rashin tsaro kalubalen rashin tsaro a hukumomin tsaron rashin tsaron tsaro a kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka hana jiharsa sakat ba baki ba ne, ’yan cikinta ne.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Ya ce tuni gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro mallakin jihar mai suna Katsina Community Watch Corps, inda aka debi matasa daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaron domin a dakile ta tun daga tushe.
DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Malaman firamare sun janye yajin aiki a AbujaKatsina dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga, inda mutane dauke da makamai kan kai farmaki kan kauyuka su kashe mutanen gari sannan su dauki wasu domin karbar kudin fansa. Sai dai a ’yan kwanakin nan jihar ta dan samu saukin hare-haren.
A cewar Gwamnan, akasarin maharan ba baki ba ne, a yankunan danginsu suke, inda ya ce amfani da mutanen yankin na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matasalar tun daga tushe.
Ya ce a sakamakon haka, an sami nasarar kama mutane da dama da ke samar wa da ’yan bindigar kayayyaki da kuma bayanan sirri.
Radda ya ce, “Ba wai cewa muke an ga bayan matsalar tsaro gaba dayanta ba, saboda har yanzu a kan samu hare-hare jifa-jifa, amma dai yanzu an samu sauki.
“A baya akwai wadanda suke tunanin gaba daya jihar ma ta koma hannun ’yan ta’addan saboda kashe-kashen da ake yi a ko ina. Amma wannan tunanin ya saba da abin da yake a zahiri.
“Dalilinmu na kirkirar sabuwar rundunar tsaro ta jiha shi ne mu taimaka wa sauran jami’an tsaro a ayyukansu. Mun dauki mutane daga dukkan yankunan da ke da matsalolin tsaro saboda su suka fi sanin yankunansu da ma mutanen cikinsa fiye da kowa.
“Mazauna wadannan yankunan sun san iyayen ’yan bindigar nan da kakanninsu, saboda ba baki ba ne. wannan ne sirrin samun nasararmu, har muke iya zuwa mu farmake su a har a maboyarsu. Dole sai da dan gari a kan ci gari,” in ji Gwamnan na Katsina.