Ma’aikatar Tsaron Amurka Ta Pentagon Ta Yi Furuci Da Hasarar Da Harin Iran Ta Janyo Mata
Published: 12th, July 2025 GMT
Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi furuci da cewa hakika an lalata sansanin sojin saman Amurka na Al Udeid na Qatar
Kakakin ma’aikatar tsaron Amurka Sean Parnell ya yi furuci da cewa: Makami mai linzami na Iran da aka kai hari da shi kan sansanin jiragen sama na Al Udeid da ke Qatar, a harin da Iran ta kai a watan Yunin da ya gabata ya janyo barna.
Sanarwar ta Pentagon ta zo ne bayan da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya wallafa hotunan tauraron dan adam da ke nuna irin barnar da harin ya janyo wanda shugaban Amurka Donald Trump ya musanta a lokacin.
A cewar hotunan tauraron dan adam da kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya yi nazari a ranar Juma’a, harin da Iran ta kai kan sansanin Al Udeid da ke Qatar ya yi kamari kuma ya afkawa wani gida mai dauke da kubba mai kusurwa uku da Amurkawa ke amfani da su wajen samun amintattun hanyoyin sadarwa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fiye Da Falasdinawa 60 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i Kadan
Ma’aikatar kiwon Lafiya ta Falasdinawa ta sanar a jiya Juma’a cewa; An kai gawawwakin shahidai 61 zuwa asibitocin yankin Gaza, a cikin sa’oi 24.
Ya zuwa yanzu adadin mutanen Gaza da su ka yi shahada tun daga 2023 sun kai 57,823, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 137,887.
Su kuwa Falasdinawan da sojojin HKI su ka kashe a wurin karbar kayan agaji sun kai 788, sai kuma wasu 5,199 da su ka jikkata.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta kuma bayyana cewa da akwai wasu dubban Falasinawa shahidai da suke kwance a karkashin baraguzai, kuma rashin kayan aiki ba zai sa a isa inda suke ba.