Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
Published: 23rd, July 2025 GMT
Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata.
Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata 22 ga watan Yuli 2025, aka gudanar da taron tawagogin kasashen uku.
Mahalarta taron a karkashin inuwar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, sun tabbatar da aniyar kasashensu na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da yin musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar.
Sun kuma jaddada muhimmancin ci gaba da wannan shawarwari domin biyan muradun kasashen uku wajen tinkarar manufofin kasashen yamma, musamman takunkuman Amurka.
Tawagogin sun amince su ci gaba da bude hanyoyin karfafa alakokinsu da kuma ci gaba da gudanar da taruka a nan gaba a matakai daban-daban a cikin makonni masu zuwa, a wani bangare na abin da suka bayyana da “kokarin hadin gwiwa na tallafawa zaman lafiyar yankin da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
APC Ta Zabi Kamilu Sa’idu A Matsayin Dan Takarar Kaura Namoda Ta Kudu A Zamfara
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zabi Hon. Kamilu Sa’idu (Wamban Kasuwar Daji) a matsayin dan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kaura Namoda ta Kudu da za a yi ranar 16 ga Agusta, 2025.
A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce Kamilu ya fito ne ba tare da hamayya ba bayan janyewar wasu ‘yan takara uku Bashir Muhammad Madaro (Walin Kurya), Anas S/Fada, da Alhaji Ashiru Hamisu Habibu—a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a makarantar firamare ta Kasuwar Daji.
Sanarwar ta ce, ‘yan takarar ukun sun sauka ne domin nuna goyon bayansu ga Kamilu Sa’idu inda suka yi alkawarin samun nasararsa da na jam’iyyar a zabe mai zuwa.
Ta ce an zabo wakilai 30 daga gundumomi shida na mazabar Kagara, Dan-Isa, Sakajiki, Kurya, Kyambarawa, da Banga — ya tabbatar da takararsa gaba daya.
Kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na kasa, karkashin jagorancin Barista Babande B. Imam ne ya jagoranci gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar, wanda a hukumance ya ayyana Kamilu Sa’idu a matsayin dan takarar jam’iyyar APC bayan da wakilan unguwanni suka amince da shi.
Barista Babande ya bayyana cewa dan takarar ya cika dukkan sharuddan tsarin mulki na jam’iyyar, kuma an tabbatar da shi a gaban jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), karkashin jagorancin kwamishina Dr. Muhammad Isah.
Bayan wannan sanarwa, shugaban kwamitin shari’a, Isah Halilu Ahmad, ya bayyana cewa idan akwai wani mai korafi dangane da sakamakon zaben fidda gwani ya fito yayi, kuma ba a sami wand ya gabatarda wani korafi ba domin duka masu neman takara da wakilai sun tabbatar da gamsuwarsu da tsarin.
Daga nan sai ya tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci, ba tare da wani magudi ba.
An gudanar da zagaye da manyan jagororin jam’iyyar da suka hada da shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Hon. Tukur Umar Danfulani; Sakataren, Hon. Ibrahim Umar Dangaladima; Mataimakin shugaban kungiyar Alh. Hassan Marafa Damri da halartar jami’an tsaro da jami’an INEC.
REL/AMINU DALHATU.