A wani ɓangare na bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Afirka, Shugaban

Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mr. Ola Olukoyede, ya yi gargaɗi kan barazanar da ke ƙara ƙamari na damfara ta hanyar kuɗaɗen zamani da kuma zuba jari na bogi a Najeriya da sauran sassan nahiyar.

 

Mr. Olukoyede ya bayyana hakan ne a yayin bukin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Afirka a wajen wani taron tattaunawa da aka gudanar a ofishin EFCC na shiyyar Kaduna.

 

Darakta na riko na shiyyar Kaduna, Bawa Usman Kaltungo wadda ya wakilici Shugaban EFCC ya bayyana cewa nahiyar Afirka na ci gaba da fama da mummunar illar cin hanci da rashawa, musamman ta hanyar fitar da kuɗaɗen haram zuwa ƙasashen waje, wanda ya ce ya zama babban cikas ga ci gaban ƙasashen nahiyar.

 

A cewarsa, Afirka na asarar biliyoyin daloli duk shekara ta hanyar waɗannan haramtattun kudade, inda wanke kuɗi ke zama mafi yawa a cikin irin waɗannan laifuka.

 

Sai dai kuma, Mr. Olukoyede ya jaddada cewa wata sabuwar barazana da ke ƙara yawaita ita ce damfara ta hanyar kuɗaɗen zamani da na’ura, kamar su cryptocurrencies da digital tokens.

 

“Kuɗaɗen zamani da kansu ba laifi ba ne,” in ji shi. “Amma amfani da su ta hanyar yaudara ko rashin bin doka shi ke mayar da su kayan aikata laifi. Abin takaici, masu laifi sun fara amfani da wannan fasaha wajen ɓoye kuɗaɗen sata, kaucewa bincike, da kuma aiwatar da shirye-shiryen zuba jari na bogi.”

 

Shugaban EFCC ya ce akwai ’yan siyasa da suka fara ɓoye dukiyar da suka sata ta hanyar cryptocurrency don kaucewa kamun hukumar. A cewarsa, digital wallets na amfani wajen adana kuɗaɗen da ba a iya bayyana asali, kuma ana amfani da fasahar blockchain wajen biyan kuɗin ayyuka marasa tushe.

 

Sai dai ya jaddada cewa EFCC ta samu ci gaba mai ma’ana wajen bankado da gurfanar da masu aikata irin waɗannan laifuka, inda ya ambaci nasarar da aka samu a bincike da gurfanar da shari’ar damfara ta CBEX.

 

“Damfara ta kuɗaɗen zamani da zuba jari ba sabbin ƙalubale ba ne ga EFCC,” in ji shi. “Ta hanyar amfani da basira da horarwa, muna samun nasarori a aikace.”

 

Ya kuma bayyana damuwa kan yadda damfara ta hanyar zuba jari kamar Ponzi scheme ke yaduwa a fadin Afirka, yana mai cewa masu yaudara na amfani da halin tsananin bukata da rashin sani na masu zuba jari don damfararsu.

 

Ya ce duk wata hanyar amfani da mutane da nufin amfana da su ta yaudara laifi ce, duk da irin tsarin da aka ɗaura mata.

 

Mr. Olukoyede ya yi kira ga jama’a da su guji yanke shawarar zuba jari ba tare da bincike da tabbaci ba, yana mai cewa mafi yawan mutanen da ake damfarawa su ne waɗanda ba sa kai rahoton ababen da ke da alamun damfara har sai da suka rasa kuɗaɗensu.

 

“Babu wata damfara ta zuba jari da za ta yi nasara ba tare da sakacin masu zuba jari ba,” in ji shi. “Ya zama wajibi a waye kai, a nemi sani, kuma a dauki matakan kariya tun da wuri.”

 

Ya sake jaddada cewa EFCC za ta ci gaba da haɗin gwiwa da dukkan masu ruwa da tsaki don hana da kuma binciken irin waɗannan laifuka, yana mai cewa faɗakarwa da wayar da kai na da muhimmanci matuƙa.

 

“Akwai buƙatar ilimi da fahimta,” ya ƙara da cewa. “Wannan dandalin tattaunawa wata dama ce ta musayar ra’ayi da fitar da hanyoyin warware wannan matsala. Masana su bayyana wa mahalarta ainihin yadda kuɗaɗen zamani ke aiki, don a rufe kofar da masu damfara ke amfani da ita.”

 

A ƙarshe, Mista Olukoyede ya buƙaci mahalarta taron da su yi magana cikin gaskiya da faɗakarwa, yana fatan taron zai haifar da fahimta mai zurfi da matakan haɗin gwiwa wajen yaƙi da wannan barazana.

COV: Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Damfara Gargadi Hanyar Jari Kuɗaɗen

এছাড়াও পড়ুন:

EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC
  • EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi
  • Kwamandan Sojin Iran Ya Jaddada Kare Kan Iyakokin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Sauye-sauyen Tinubu Suna Taimaka Wa Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya — Minista
  • UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
  • EFCC Ta Kama Ƴan Ƙasashen Waje 146 Kan Laifukan Zambar Kuɗaɗe
  • Sojojin Yemen Sun Nutsar Da Jirgin Ruwan “Eternity” Dake Hanyar Zuwa HKI
  • Mai Tsoron Ta Mutu, Shi Yake Maho
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce; An Rusa Hanyar Tattaunawa da Iran Kan Shirin Na Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya