Mataimakin Shugaban Kasar Iran Na Farko Ya Jaddada Wajabcin Damawa Da Kowane Bangare A Fagen Jagorantar Kasar Iran
Published: 14th, July 2025 GMT
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya jaddada cewa; Ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa akan fagen yadda al’amura zasu karfafa
Mataimakin shugaban kasar na farko na kasar Iran Mohammed Reza Aref ya bayyana cewa: Babu wani bambanci tsakanin diflomasiyya da fannin, inda ya ce har yanzu ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa kan hanyoyi kyautata gudanar da madafun iko.
A yayin ganawarsa da malaman jami’ar Shariff ta fasahar kere-kere, Aref ya yaba da irin rawar da al’ummar Iran suka taka a yakin kwanaki 12 da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dorawa Iran, inda ya ce: Matsayin al’ummar Iran da kasancewarsu a fagen kare kasar ya kasance mai karfi wajen yakar makiya, saboda dabarun makiya shi ne cewa bayan harin da aka kai wa bangaren soja na Iran, al’ummar Iran za su dauki matakan yaki da gwamnati Jamhuriyar Musulunci amma sai al’umma suka dauki matakin wargaza makircin makiya ta hanyar jaddada goyon bayansu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.
Ya kara da cewa: A halin yanzu Iran tana da kyakkyawar damar bunkasa kimiyya ta fannin fasahar kere-kere da tsaro ta yanar gizo, kuma an kafa kwamitin bayani don tabbatar da yadda ya kamata a raba aiki tsakanin bangarorin gwamnati da masu zaman kansu, musamman jami’o’i ciki har da Jami’ar Fasaha ta Sharif.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin
“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.”
“Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!”
A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar Sin, tare da hada kai da kasar Sin da ma sauran baki ’yan kasuwa wajen kyautata tsarin samar da kayayyaki na duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp