Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah Wadai Da Kakaba Takunkumi Kan Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya
Published: 11th, July 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi tsokaci kan takunkumin Amurka ta kakaba kan jami’ar Majalisar Dinkin Duniya da cewa: Ba za a iya murkushe gaskiya ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi tsokaci kan takunkumin da Amurka ta kakaba wa wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese.
A cikin wani rubutu a dandalin “X” a ranar Juma’a, Baqa’i ya bayyana cewa: “Ba za a iya murkushe gaskiya ba.” Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu, Francesca Albanese, ta fuskanci takunkumi da girman kai saboda fallasa gaskiya da kuma tsayin daka kan laifukan kisan kare dangi, mamaye yankunan Falasdinawa da nuna wariyar al’umma.
A cikin sakonsa, Baqa’i ya bayyana cewa: Wannan hukuncin na takunkumi ya zo daidai da karbar bakwancin mai laifin yaki da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, Benjamin Netanyahu da ake nema ruwa a jallo yake birnin Washington na Amurka, ya kara da cewa: “A yau Amurka tana nuna munafunci a fili, kuma duniya ta shaida hakan.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta raba zunzurutun kuɗi naira miliyan 63.4 ga iyalan jami’anta 84 da suka rasa rayukansu a bakin aiki.
Rundunar ta raba kudin ne a ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da kuma tsarin kula da lafiyar iyali na Sufeto Janar na ’yan sanda.
An gudanar da rabon kuɗin ne a ranar Alhamis a Maiduguri babban birnin jihar kamar yadda Kakakin rundunar a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa.
A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, wanda ya wakilci Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, shi ne ya gabatar da takardun cakin kudin ga iyalan waɗanda suka ci gajiyar tallafin.
“Harkokin da suka shafi jami’anmu da iyalansu ya kasance babban fifiko ga rundunar,” in ji CP Abdulmajid yayin taron.
Ya ce wannan shiri na nuna tausayi da rikon amana, da kuma jagoranci mai nagarta daga Sufeto Janar wajen girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyalan da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya dace, musamman wajen tallafa wa ilimi, kiwon lafiya, da jin daɗin rayuwar iyalansu gaba ɗaya.
Ya yaba wa Sufeto Janar bisa ci gaba da tsare-tsaren jin daɗin jami’an rundunar, yana mai bayyana su a matsayin muhimman hanyoyin da ke samar da agaji da kwanciyar hankali ga iyalan waɗanda suka rasa masoyansu.
A nata jawabin a madadin iyalan da suka amfana, Misis Nana Goni ta nuna godiya ga Sufeto Janar bisa goyon bayan da ya bayar, tana mai tabbatar da cewa za su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata don inganta rayuwar iyalansu.
Rundunar ta bayyana cewa wannan rabon tallafi ya sake tabbatar da jajircewarta wajen kula da walwala da mutuncin jami’anta da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma.