Amurka Ta Rage Wa’adin Bizar ‘Yan Nijeriya Zuwa Wata Uku
Published: 11th, July 2025 GMT
Amurka ta bayyana dalilin sabunta manufofin, tare da lura da cewa “an tsara sharuddan bizar Amurka da ka’idoji domin kare tsarin shige da fice na Amurka.”
Ofishin jakadancin ya kara da cewa “wadannan ka’idoji sun dogara ne kan ma’aunin fasaha da tsaro na duniya.”
A cewar ofishin jakadancin Amurka yana aiki tare da hukumomin Nijeriya domin cimma wadannan matakan.
Sanarwar ta ce “Tawagar Amurka tana aiki tare da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da cewa Nijeriya za ta iya cika sharuddan.”
Misalin wannan sabon tsari ya hada da “Takardun tafiye-tafiye masu aminci: tabbatar da cewa kasashe suna ba da amintattun takaddun balaguro tare da ingantattun bayanan matafiyi, Kada aikin gudanar da Bisa ya wuce lokacin da aka dauka:.”
Duk da sabbin takunkumin, ofishin jakadancin ya sake jaddada alakar diflomasiyya da Nijeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Amurka na mutunta dangantakarta da Nijeriya da dadewa, kuma tana ci gaba da jajircewa wajen fadada hadin gwiwarmu bisa mutunta juna, da muhimman batutuwan tsaro, da damar tattalin arziki, tare da tabbatar da tsaron kasashen biyu.”
Har ila yau, ofishin jakadancin ya nuna goyon bayansa ga sauye-sauyen da Nijeriya ke ci gaba da yi, inda ta ce, “Mun yaba da kokarin da hukumomin shige da fice da na tsaro na gwamnatin Nijeriya ke yi na ganin sun cika ka’idoji kyawawan ayyuka na kasa da kasa.”
An shawarci matafiya na Nijeriya da su bi ka’idojin bizar.
“An bukaci matafiya ‘yan Nijeriya da su mutunta tare da kiyaye sharuddan bizarsu, kuma su tabbatar da ingantattun takaddun balaguro, kuma na zamani.”
Ofishin jakadancin ya karkare da jaddada huldarsa da jama’a da gwamnatin Nijeriya.
“Amurka ta kasance amintacciya a cikin zurfafa dangantakar jama’a da Nijeriya ta hanyar kasuwanci, ilimi da mu’amalar al’adu.
“Muna fatan ci gaba da hadin gwiwa a dukkan matakai tare da jama’ar Nijeriya da jami’an gwamnati don tabbatar da tafiya cikin aminci da doka tsakanin Amurka da dukkan kasashe,” in ji ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: jakadancin ya da Nijeriya tabbatar da Nijeriya da
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Tabbatar Da Cewa Tana Iya Yakar Amurka Da HKI A Lokaci Guda
Tsohon babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci wato IRGC ya bayyana cewa a yakin da JMI ta fafata a cikin watan da ya gabata , ya tabbata cewa JMI tana iya yaki da Amurka da HKI a lokaci guda.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Mohsen Rezaei, yana fadar haka a lokacinda wata talabijin ta cikin gida take hira da shi a jiya Talata .
Labarin ya kara da cewa Janar Rezaei ya taba rike mukamin babban kwamandar rundunar IRGC jim kadan bayan nasarar juyin juya halin musulunci a shekara 1979.
Yace: Shahid Janar Qasem Sulaimani, Babban kwamandan rundunar Qudus ne ya fara furta zancen cewa , Iran tana da karfin fuskantar Amurka. Wannan kuma ya tabbata a yankin kwanaki 12 da aka dorawa kasar.
A halin yanzu dai Janar Rezaei yana cikin wadanda suke bawa Jagoran juyin juya halin musulunci shawara a kan al’amuran tsaro da siyasa.