Eritrea ta gargadi Habasha game da yunkurin kafa tashar jiragen ruwa a cikin yankinta
Published: 23rd, July 2025 GMT
Wata sabuwar tashin-tashina ta sake kunno kai a yankin kahon Afirka a daidai lokacin da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya yi gargadi kai tsaye ga firaministan Habasha Abiy Ahmed, inda ya yi kashedin sake kaddamar da wani yaki.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Habasha ke kokarin shiga bangaren ruwa Eritra da kuma tabarbarewar dangantakar bangarorin biyu tun bayan rikicin Tigray.
A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan telebijin, shugaba Afwerki ya yi gargadin cewa adadin yawan jama’ar Habasha ba zai tabbatar da nasarar soji ba, yana mai nuni da dabarun yakin da Habasha ta yi amfani da su a yakin da ya gabata, yana mai cewa duk da yawan sojojinta amma bata samu nasara ba.
Afwerki ya kira matakin na Abiy a matsayin “rashin hankali” tare da danganta hakan da matsalolin siyasar cikin gidan Habasha. Ya kuma nanata cewa Eritrea ba za ta amince da keta hurumin kasarta ba, ya kuma bukaci Habasha da ta warware matsalolin cikin gida kafin ta yi la’akari da daukar mataki a kan waje.
Kasar Habasha wadda ita ce kasa mafi yawan al’umma a gabashin nahiyar Afirka, ta dade tana neman shiga Tekun Bahar Maliya, ayyin da Eritiriya take yin matukar kaffa-kaffa da wannan manufa ta Habasha.
Kasashen Eritrea da Habasha sun jima suna zaman doya da manja tun bayan da Eritrea ta kwashe shekaru 30 tana yakin neman ‘yencin kai da mulkin Habasha, wanda ya kai ga samun ‘yancin kai a 1993.
Rikicin da ya fi kamari ya faru ne daga 1998 zuwa 2000, lokacin da wani mummunan yakin kan iyaka ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 100,000. Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya hannu a kanta a cikin 2018, amma babu wani tabbaci kan ci gaba da wanzuwar wannan yarjejeniya.
Habasha tana da yawan jama’a miliyan 130, Eritrea miliyan 3.5 kawai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka.
“Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem.
Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen duniya da gaza aiwatar da dokokin kasa da kasa, yana mai cewa, “Shiru da kasashen duniya suka yi, abin Allah wadai ne ga gwamnatocin kasashen duniya, musamman na kasashen musulmi da larabawa.
Da yake ishara da kiraye-kirayen baya-bayan nan da kasashe sama da ashirin suka yi na a dakatar da yakin, Sheikh Qassem ya yi ishara da cewa irin wadannan kalamai da cewa ba su isa ba ko kadan, Ya ce, “bai isa ba a ce kasashe 25 sun yi kira da a dakatar da yakin Gaza, wannan furucin kadai bai wadatar ba.
Sheikh Qassem ya yi kira da a kakaba takunkumi kan “Isra’ila”, da gurfanar da su a gaban shari’a, da kuma dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.