Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Matsayin Jihar A Zaman Nazarin Kundin Tsarin Mulki
Published: 12th, July 2025 GMT
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya gabatar da matsayar Jihar Kaduna a zaman jin ra’ayin jama’a dangane da gyaran kundin tsarin mulkin shekarar 1999.
An gudanar da taron ne a gidan Gwamnati na General Hassan Katsina da ke Kawo, a garin Kaduna, a matsayin wani bangare na ci gaba da shirin gyaran kundin tsarin mulki da Majalisar Wakilai ta kasa ke jagoranta.
Wannan zaman jin ra’ayi da aka ware a matsayin Cibiyar ta daya, ya hada da jihohin Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa.
Taron ya tara shugabanni daga fannoni daban-daban ciki har da ’yan siyasa, da sarakuna da kuma wakilan kungiyoyin fararen hula, domin tattauna batutuwan da suka shafi sauye-sauyen kundin tsarin mulki.
Cikin manyan bakin da suka halarci taron sun hada da Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe, wacce ta wakilci Gwamna Sanata Uba Sani, da Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa da Mataimakin Jagoran ’Yan Adawa na Majalisar Wakilai ta Kasa, Rt. Hon. Aliyu Sani Madaki.
An kuma samu halartar sarakuna da suka hada da Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje, wadanda suka bayar da gudummawa ta hikima da goyon baya a wajen taron.
A lokacin da yake gabatar da jawabi, Rt. Hon. Liman ya bayyana muradun al’ummar Kaduna dangane da batutuwan gyaran kundin tsarin mulki, inda ya jaddada bukatar sauya dokokin tsarin mulki domin su dace da zamani, da tabbatar da adalci, da daidaito da ingantaccen mulki.
“Gyaran kundin tsarin mulki na 1999 mataki ne mai muhimmanci wajen karfafa ginshikin dimokuraɗiyyar Najeriya. Jihar Kaduna za ta ci gaba da taka rawa wajen bada gudummawar gina tsarin mulki da zai kunshi kowa da kowa.” Inji shi.
Taron jin ra’ayoyin na shiyyar Arewa yana ba da dama ga ’yan kasa, kungiyoyi da wakilan jama’a su bayyana ra’ayoyinsu da kuma gabatar da takardun bayani kan batutuwan kasa da suka shafe su.
Wannan wani muhimmin mataki ne na tabbatar da cewa tsarin gyaran kundin mulki yana tafiya ne bisa tsari mai kunshe da ra’ayin kowa da kowa daga sassa daban-daban na kasar.
Shamsuddeen Munnir Atiku
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Matsaya gyaran kundin tsarin mulki Jihar Kaduna
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.
Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.
Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.
A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.
“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.
Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.
Tinubu ya kuma yaba wa masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.
Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.
Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.
Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.
Daga Bello Wakili