Ban da haka, bayan da aka tsara “shirin shekaru 5”, yana da muhimmanci a aiwatar da shi. A kasar Sin, bayan da aka gabatar da wani “shiri na shekaru 5”, dole ne a aiwatar da shi yadda ake bukata. Kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar za su tsara salon aiwatar da dukkan ayyuka, da raba su ga sassa da yankuna daban-daban, don a aiwatar da su a matakai daban daban.

Bayan haka, hukumomi daban daban su kan gudanar da ayyukan sa ido a tsakiyar wa’adin shirin, kuma za a tantance ainihin sakamakon da aka samu bayan karewar shirin.

Ta wadannan halayen musamman, za a iya ganin abubuwan da za su tabbatar da aiwatar da shirin na raya kasa: Na farko, kokarin kare muhimman muradun jama’a, da tabbatar da yanke shawara ta wata hanya mai dacewa, kuma bisa tsarin dimokuradiyya. Na biyu, yin amfani da tsare-tsaren shari’a wajen tabbatar da ingancin shirin da aka tsara, da mai da shi karkashin sa ido da aka yi masa. Na uku, tun daga gwamnatin tsakiya zuwa kananan hukumomi, dole ne a aiwatar da shirin raya kasa a tsanake, domin tabbatar da cimma burin da aka sanya a gaba. A cikin wadannan abubuwa, ana iya ganin ruhin dimokuradiyya da bin doka da oda, da kuma yanayin aiki na mai da hankali, da nuna sanin ya kamata, wadanda suka kasance tushen ci gaban kasar Sin.

A cewar mista Peterside, ta hanyar koyi da fasahohin kasar Sin, Najeriya za ta iya cin gajiyar dimbin albarkatun kasa da take da su, don tabbatar da cikar burinta na raya tattalin arziki. Ni ma na yi imanin cewa, Najeriya za ta iya yin hakan, tare da samun biyan bukata. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: a aiwatar da tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban

Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka halaka yayin da wasu 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da aka kai musu a arewacin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka sheka lahira sannan wasu akalla 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da ‘yan gwagwarmaya suka kai a Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. Har yanzu wani sojan Isra’ila ya bace kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka ruwaito.

Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da s’yan gwagwarmaya suka tayar da bam a cikin wata motar sojin Isra’ila mai sulke dauke da sojoji, sannan suka nufi wani mutum-mutumi da ke dauke da harsashi da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi.

Hare-haren dai sun auka ne kan dakarun ceto na Isra’ila da suka garzaya zuwa wurin, yayin da mazauna birnin Ashkelon suka ji karar fashewar wani babban bam, a cewar shafukan yanar gizo na Isra’ila, inda suka ce daya daga cikin wadanda suka jikkata wani babban jami’i ne.

Sojojin da aka kai wa harin na sashen injiniyan Yahalom ne, wanda ke da alhakin yin tarko da kuma tayar da bama-bamai a gidajen Falasdinawa a zirin Gaza, a cewar wakilin Al Jazeera na Falasdinu, Najwan Samri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing
  • Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Amince Iran ta Kai Hare-Hare Kan cibiyoyin Sojojinta Guda Biyar
  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Idan Tanaso
  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliya Kasar Idan Tanaso
  • Iran Ta Tabbatar Da Cewa Tana Iya Yakar Amurka Da HKI A Lokaci Guda
  • Xi: Ana Kokarin Rubuta Sabon Babi Na Zamanantar Da Sin A Lardin Shanxi
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
  • Amurka Ta Soke Dokar Da Ta Tabbatar Da Hai’at Tarirusham Cikin Jerin Kungiyoyin Yan Ta’adda