An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos
Published: 10th, July 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa unguwar Qua da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato.
Adadin waɗanda aka kashe mutum 32 da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara suna cikin wata mota ƙirar bas mai kujeru 18 daga unguwar Basawa da ke Ƙaramar hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna, domin halartar bikin aure a lokacin da suka haɗu da maharan.
Da yake gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban babbar kotun jihar, lauya mai shigar da ƙara, S.I. Ikutanwa, ya nemi izinin kotun domin waɗanda ake zargin su ɗaukaka ƙara kan tuhume-tuhume huɗu da ake yi musu.
Sai dai lauyan da ke kare waɗanda ake zargin Garba Pwol, ya ƙi amincewa da buƙatar ƙarar, inda ya ce biyu daga cikin mutum 22 ƙananan yara ne, wanda hakan ya sa tuhume-tuhumen ba su da tushe.
A cewar lauyan da ke kare waɗanda ake zargin ’yan shekaru 13 ne da kuma 17, kuma doka ba ta yarda a gabatar ƙananan yara a irin wannan shari’ar ba. Lauyan da ke kare waɗanda ake ƙara ya buƙaci kotun da ta ba shi lokaci domin shigar da ƙara.
Da yake mayar da martani ga lauyan waɗanda ake tuhuma, lauyan mai shigar da ƙara ya ce, tun da biyu daga cikin waɗanda ake zargin ’yan ƙasa da shekaru 18 ne a cire sunayensu, sannan a bar sauran mutum 20 da ake tuhuma su amsa tuhumar.
Da yake tsokaci kan sharia’ar ga ɓangarorin biyu da suka gabatar, alƙalin kotun, Mai shari’a Boniface Ngyon, ya ce zai fi kyau kada a shigar da ƙarar nasu ranar Alhamis, maimakon haka za a yi gyara a ranar Juma’a, ban da ƙananan yara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: waɗanda ake zargin shigar da ƙara ƙananan yara da ake zargin
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza
Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 24 daga cikin dare zuwa wayewar garin ranar Alhamis a Zirin Gaza.
Majiyoyi a yankin sun shaida wa gidan talabijin na Al-Jazeera cewa akasarin mutum 24 din da aka kashe a zirin na Gaza mata ne da kananan yara.
NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Ba Tinubu kaɗai ne ya sa Buhari ya ci zaɓe a 2015 ba – Boss MustaphaAkasarin mutanen dai an kashe su ne a tsakiya da kudancin zirin na Gaza.
Ma’aikatan lafiya a asibitin Al-Aqsa da ke Gaza sun ce a yankin Deir el-Balah kawai akwai Falasdinawa 13 da aka kashe sannan an jikkata wasu da dama.
Gabanin nan ma, Isra’ila ta kashe mutum hudu a harin da ta kai sansanin ’yan gudun hijira na Bureij, shi ma wanda ke tsakiyar Gaza.
Sama da mutum 700 ne Isra’ila ta kashe Falasdinawa 700 da ke kokarin karbar tallafi a wuraren karbar tallafi na Gidauniyar GHF wanda Amurka da Isra’ilar suke goya wa baya tun lokacin da aka kaddamar da shi a watan Mayu.
Daga cikin mutanen dai akwai yara kanana da dama, ciki har da wani jariri dan kwana 10 da haihuwa.