Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
Published: 23rd, July 2025 GMT
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, da shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Huning, sun gana da shugaban majalisar dattijan kasar Madagascar Richard Ravalomanana.
Yayin ganawar, Zhao Leji ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin kokari tare da Madagascar, don sa kaimi ga raya hadin gwiwa, da sada zumunta a tsakaninsu, da samar da gudummawa ga raya kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamani.
Yayin ganawar tsakanin Wang Huning da Ravalomanana, Wang ya bayyana cewa, Sin da Madagascar hakikanin abokan juna ne, yayin da ake zamanintar da kasashen. Kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, na fatan yin mu’amala tare da majalisar dattijai ta kasar Madagascar, wajen taimakawa raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, Ravalomanana ya bayyana cewa, majalisar dattijan kasar Madagascar, na fatan yin kokari tare da kasar Sin, wajen inganta mu’amala a tsakanin hukumomin kafa dokokin kasashen biyu, don sa kaimi ga raya hadin gwiwar kasashen biyu, a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, da harkokin kananan hukumomi kasar da sauransu. Kana yana fatan kara yin mu’amala da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, a fannin sarrafa harkokin kasa, da kuma sa kaimi ga daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Madagascar
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki.
A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp