Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21
Published: 22nd, July 2025 GMT
Yuro biliyan 4
Yen biliyan 15 (na Japan)
Tallafin dala miliyan 65
Kuma aron cikin gida ta hanyar sayar da hannun jarin gwamnati (bond) na kusan Naira biliyan 757.
Har ila yau, akwai shirin tara kuɗi har dala biliyan 2 ta hanyar takardun lamuni da za a fitar cikin ƙasa amma a kuɗin ƙetare.
Shugaban kwamitin kasafi, Sanata Olamilekan Solomon, ya ce wannan amincewa tsarin doka ce kawai, domin an riga an haɗa bashin cikin tsare-tsaren kasafin kuɗi da MTEF tun da farko.
Sanata Sani Musa (Niger Ta Gabas) ya bayyana cewa wannan shiri ba na shekara ɗaya ba ne, amma zai shafi rabon kuɗi na tsawon shekara shida, yana mai jaddada cewa Nijeriya ba ta taɓa gazawa wajen biyan bashinta ba.
Shugaban kwamitin Bankuna da harkokin kuɗi, Sanata Adetokunbo Abiru (Lagos Ta Gabas), ya tabbatar da cewa dukkan bashin na bin ƙa’idojin dokar kula da bashi da ta ɗabi’un da suka dace da dokar kuɗi.
Sai dai Sanata Abdul Ningi (Bauchi Ta Tsakiya) ya nuna damuwa game da ƙarancin bayani da ake da shi kan yadda za a raba bashin da kuma hanyoyin da za a biya su.
Ya nemi a bayyana adadin da kowace jiha ko hukuma za ta samu, da kuma amfanin bashin domin a iya bayyana wa al’umma gaskiya.
A cikin jerin ayyukan da za a aiwatar da kuɗin akwai:
Gina layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri
Tsarin wutar lantarki da sadarwa na zamani
Harkokin tsaro
Noma da aikin gidaje
Sanata Victor Umeh (Anambra Ta Tsakiya) ya goyi bayan shirin, yana mai bayyana cewa wannan ne karon farko da ake ware dala biliyan 3 domin gina layin dogo a gabashin Nijeriya.
Mataimakin Shugaban Majalisa, Barau Jibrin ya yabawa kwamitin bisa aikin da ya yi, yana mai cewa “dukkan yankunan ƙasa na cikin shirin kuma hakan na nuna cewa Agenda ta ‘Renewed Hope’ tana aiki.”
Majalisar ta jaddada cewa duk wani kuɗin da za a fitar dole ne a yi amfani da shi ne kawai wajen ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma, bisa tanadin dokar kuɗin gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
– Emmanuel Adegbola Aina – AIG na wucin gadi, sashen leƙen asiri
– Omolara Ibidun Oloruntola
– Hassan Abdu Yababet – CP, Kwalejin ‘Yan Sanda Jos
– Bretet Emmanuel Simon – CP Jihar Taraba
– Enyinnaya Inonachi Adiogu – CP, FCID, Gombe
– Aminu Baba Raji – CP, FCID Alagbon
– Mohammed Mu’azu Usman – CP, Tashoshin Gabas, P/Harcourt
– Festus Chinedu Oko – AIG na wucin gadi, sashen DLS, Hedkwatar
– Ronke Nurat Okunade – CP, SFU FCID Annex, Lagos
Kazalika, PSC ta amince da:
– Ɗaga darajar DCP 16 zuwa CP
– Ɗaga darajar ACP 27* zuwa DCP
– Ɗaga CSP 145 zuwa ACP, ciki har da likitoci, ma’aikatan lafiya, injiniyoyi na jiragen sama, da limamai
– Ɗaga SP 29 (na musamman na sashen kimiyyar sadarwa da aikace-aikace da AFIS) zuwa CSP
– Ɗaga DSP 38 zuwa SP
Wani ACP ɗaya bai samu damar halarta ba, don haka ba a ɗaga darajarsa ba.
Sabbin CP 16 sun haɗa da:
– Uduak Otu Ita
– Sheikh Mohammed Danko
– Charles Ezekwesiri Dike
– Nnana Oji Ama (FCID Intelligence)
– Gabriel Onyilo Eliagwu
– Abiola Reuben Olutunde
– Yakubu Useni Dankaro
– Michael Adegoroye Falade
– Aina Adesola
– Umar Ahmed Chuso
– Emefile Tony Osifo
– Innocent Ilogbunam Anagbado
– Musa Mohammed Sani
– Victor Avwerosuo Erivwode (DC SEB, FCID)
– Omoikhudu Philip
– Sylvester Edogbanya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp