Ɗalibi ya ƙone budurwarsa mai tsohon ciki har lahira
Published: 12th, July 2025 GMT
Ana zargin wani ɗalibi da ke shekarar ƙarshe a jami’a da ƙona budurwarsa mai ɗauke da tsohon ciki a Jami’ar Fatakwal da ke Jihar Ribas.
Wanda ake zargin da budurwar tasa mai suna Cynthia Chukwundah, dukkansu ɗaliban ajin ƙarshe ne a jami’ar.
Ana zargin matashin ya ƙona Cynthia mai shekara 32 ne ta hanyar wata mata ruwan batir, daga bisani ta ce ga garinku nan.
Cynthia ta gamu da ajalinta ne bayan saurayinta Sunny Amadi ya yi mata wannan aika-aika a gidansu da ke layin Okoro unguwar China da ke Birnin Fatakwal.
Sojoji sun kama mai garkuwa da mutane da bindigogi Muna tunanin sayar da matatun man Najeriya — NNPCLWani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa “Abu kamar wasa suka fara cacar baki, wannan na faɗa wannan na mayar da martani kowa dai bai sanya musu baki ba, kowa kuma ya shiga ɗakinsa ya kwanta. Ƙarshe sai ya watsa mata wani sinadarin da ya ƙone ta kamar ƙunar wuta, ga ta ɗauke da tsohon ciki, ita da tsohon ciki da abin da ke cikin cikin suka mutu,” in ji majiyar.
Ya ce, “Bayan da saurayin ya yi wa Cynthia wannan aika-aika, ya sulale ya gudu, amma daga baya ’yan sanda suka kama shi a maɓoyarsa.
“Maƙwabta suka yi ƙoƙarin gaggawar kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal (UPTH ) domin a ceto rayuwarta da ta abin da ke cikin cikinta, amma rai ya yi halinsa sakamakon munanan raunuka na sinadarin da saurayin ya watsa mata a jiki da ake zato sinadarin Asid ne.”
Kakakin ’yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa rundunar tana tsare da saurayin kuma yana bayar da haɗin kai a binciken da ke gudanarwa, kuma da zarar an kammala bincike, za a miƙa shi kotu ta yi aikinta.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.
Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.
Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.
Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.
Usman Muhammad Zaria