Tsoffin Jami’an ‘Yan Sanda Sun Bukaci A fitar Da Su Daga Cikin Shirin Fansho
Published: 22nd, July 2025 GMT
Jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman a cire su daga shirin bayar da gudunmawar fansho (CPS).
An ga jami’an ‘yan sandan da suka yi ritaya a jihar karkashin kungiyar ‘yan sandan Najeriya mai ritaya (ARPON), dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar su “Shugaban kasa, NASS da IGP ya kamata a girmama ‘yan sanda su kebe ‘yan sanda daga CPS, su kafa hukumar ‘yan sanda ta fensho don gudanar da gratuity da fansho, idan CPS na da kyau haka, me ya sa AIGs da sauran su suka fice daga cikin shirin?
Da yake jawabi ga ‘ya’yan kungiyar a lokacin zanga-zangar lumana a Ilorin, shugaban kungiyar, Yakubu Jimoh, babban Sufeton ‘yan sanda mai ritaya, ya yi zargin cewa shirin yana cike da kalubale tun farkonsa.
A cewarsa jami’an da suka yi ritaya wadanda suka fada cikin tsarin fansho ya kamata a kebe su kamar wadanda suka kai matsayin Janar a rundunar.
Ya nemi kafa hukumar fansho ta ‘yan sanda mai alhakin kula da al’amuran ‘yan sanda na fansho kamar yadda ya shafi sauran hukumomin tsaro.
Jimoh ya bayyana cewa rahoton kwamitin majalisar dattijai mai kula da kafa da ayyukan gwamnati a kan kudirin dokar kafa hukumar fansho ta ‘yan sanda, wadda aka gudanar a watan Nuwambar bara ta fitar da shi, duk da cewa an gudanar da shi watanni takwas da suka gabata.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da majalisar dokokin kasar da su gaggauta bin diddigin yadda majalisar za ta bi wajen fitar da naira biliyan 758, karancin kudaden fansho da ke bin hukumomin tsaro.
A nasa bangaren, mashawarcin shari’a na kungiyar ‘yan sandan Najeriya mai ritaya Adekunle Iwalaiye, ya ce jami’an da suka yi ritaya sun cancanci a biya su fansho na rayuwa ba wai dan abin da ake jefa musu ba duk wata ba.
Ya bukaci gwamnati da ta yi aiki da bukatar wadanda suka yi ritaya, duba da irin ayyukan alheri da suka yi wa kasar nan tsawon shekaru 35.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara Yansanda da suka yi ritaya
এছাড়াও পড়ুন:
Kamfanin Amazon na shirin sallamar ma’aikata 600,000 don maye gurbinsu da mutum-mutumi
Kamfanin Amazon, wanda shi ne na biyu a yawan ma’aikata a Amurka, zai sallami ma’aikata kusan 600,000 ta hanyar maye gurbin su da mutum-mutumi nan shekaru 10 masu zuwa.
Wani rahoton takardun cikin gida na kamfanin ne ta bayyana hakan, kamar yadda jaridar The New York Times ta Amurka ta wallafa.
Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29 Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35A cewar rahoton, wannan dabarar na fitowa ne daga masu lura da ma’aikata na kamfanin da alkaluman su ke nuna cewa kamfanin na iya kauce wa ɗaukar fiye da mutum 160,000 da ake bukata a Amurka nan da shekarar 2027.
Kamfanin dillancin kaya na Amazon ya taɓa bayyana cewa amfani da mutum-mutumi zai ba shi damar faɗaɗa kasuwancinsa zuwa ninki biyu na yawan kayayyakin da yake siyarwa nan da shekarar 2033, ba tare da ƙara yawan ma’aikata a Amurka ba.
Tarin takardun da aka tattara tare da hirarraki da jaridar ta gudanar ya nuna cewa wannan sauyi zai sa kamfanin ya zama ba ya buƙatar ɗaukar fiye da mutum 600,000 a cikin shekaru goma masu zuwa.
Sai dai Amazon ya ƙi amincewa da sakamakon binciken na jaridar.
A cikin wata wasika da ta aike wa The Independent, Amazon ya ce adadin mutum 600,000 ya fito ne daga wata takarda daga sashe guda na kamfanin, wanda ba shi da alaka da ɗaukar ma’aikata.