Aminiya:
2025-10-15@21:19:08 GMT

WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka

Published: 13th, July 2025 GMT

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya sanar da dakatar da bayar da tallafin abinci a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka da ke fama da rikici.

Hakan dai na zuwa ne a sakamakon rage tallafin da Amurka ke bayarwa na kuɗi ƙarƙashin Hukumar USAID, wanda hakan ke kawo cikas ga ayyukan wannan ƙungiyar.

Za a sa zare tsakanin Amurka da Turai kan harajin kasuwanci An sanya dokar hana fita a Adamawa

Duk da cewa lokaci ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, ana hasashen kayan abinci za su isa zuwa kusan watan Satumba a mafi yawan ƙasashen da abin ya shafa, wanda hakan zai bar miliyoyin mutane masu rauni cikin halin rashin tallafin gaggawa, a cewar WFP.

“Muna yin duk mai yiwuwa don fifita ayyukan da suka fi muhimmanci wajen ceton rayuka, amma ba tare da samun goyon bayan gaggawa daga abokan hulɗarmu ba, damar mu na amsa buƙatu tana raguwa kowace rana.

“Muna buƙatar ci gaba da samun kuɗaɗe don tabbatar da ci gaba da rarraba abinci da kuma kiyaye fata,” in ji Margot van der Velden, daraktar yanki a WFP a tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

Ƙasashe bakwai ne abin ya shafa a wannan yanki, inda dakatar da ayyuka ya riga ya fara a Mauritaniya, Mali, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda ake hasashen kayan abinci za su isa na ‘yan makonni kaɗan kawai.

Alƙaluman sun nuna cewa rabon tallafi ya ragu sosai a sansanonin ‘yan gudun hijira na Nijeriya da ke Kamaru, a cewar WFP.

A cewar bayanan WFP da AP ta gani, ana hasashen lamarin zai yi tasiri kan miliyoyin mutane kai tsaye, ciki har da yara 300,000 a Nijeriya da ke cikin hatsarin shiga halin “matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki, wanda zai iya ƙara haɗarin mutuwa.”

WFP ta ce tana buƙatar dala miliyan 494 domin samar da abinci a rubu’i na biyu na shekarar 2025, amma kuɗaɗen sun ƙare gaba ɗaya, wanda hakan ya tilasta ta fifita rukunin mutane masu rauni.

A Arewa da Tsakiyar Mali, za ta fifita ‘yan gudun hijira da aka kwashe kwanan nan da kuma yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Ɗinkin Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Enugu Peter Mbah da kwamishinoninsa sun koma APC

Gwamna Peter Mba na Jihar Enugu da kwamishinoninsa da sauran mukarrabansa sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Da yake sanar da hakan a ranar Talata a garin Enugu, Gwamna Mbah ya jaddada aniyarsa ta kare muradun jihar, tare da bayyana kwarin gwiwa cewa APC za ta ba wa jihar karin damar hadin gwiwa domin samun ci-gaba.

Mbah, wanda ya samu rakiyar magabacinsa, tsohon Gwamna Ifeanyi Ugwanyi, da ’yan  majalisar dokokin jihar da takwarorinsu na Majalisar Dokoki ta Kasa ya ce sun yi ittifafkin komawa APC ne domin kara hidimta wa al’ummar jihar da kuma kare manufofinta na ci gaba.

“Bayan tsawon lokaci ana ta nazari, a yau dai, mun yanke shawarar sauya sheka daga PDP zuwa APC. Wajibi ne mu ci gaba a kan muradunmu na ci gaba.

’Yan Majalisar Tarayyar Kaduna 3 sun sauya sheka daga PDP Sakin Maryam Sanda shi ne ƙololuwar zalunci —Dangin Bilyaminu

“Na fahimci cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, abonkin tafiya ne ta fuskar manufa, kuma jajirtaccen mutun ne mai hangen nesa da ke daukar matakan da za su amfane mu a na gaba,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan shawara ce a muka dauka a dunkule — ’yan majalisar dokokin jiha da majalisar dokoki ta kasa da Majsaliar Zartaswa ta jiha daukacin shugabannin kananan hukumomi da masu rike da mukaman siyasa da kimanin kashi 80 na shugabannin jam’iyya.”

Duk da cewa ya bayyana godiya ga PDP da gudummawarta a lokacin zabensa, amma ya koka da cewa “yawanci ba a sauraron muryarmu” idan wani sha’ani ya taso da ya shafi yankin Kudu maso Gabas.

Ya bayyan kwarin gwiwa cewa hadewarsa da APC zai taimaki ci-gaban Jihar Enugu da ma Najeriya baki daya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa
  • Madugun ’yan adawar kasar Kenya, Raila Odinga, ya mutu
  • Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu
  • Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe
  • Gwamnan Enugu Peter Mbah da kwamishinoninsa sun koma APC
  • Sakin Maryam Sanda shi ne ƙololuwar zalunci —Dangin Bilyaminu
  • Kamaru: Jam’iyyun adawa sun ayyana Bakary a matsayin wanda ya lashe zaɓe
  • An Gano Gawarwaki 323 Karkashin Burabutsai Bayan Dakatar Da Bude Wuta A Gaza
  • An Kara Zaburar Da ‘Yan Arewa Game Da Muhimmancin Mallakar Katin Zabe
  • Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako