Shirin Sabunta Fata Na Tinubu Yana Samar da Damarmakin Cigaba — Minista
Published: 11th, July 2025 GMT
Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana aiwatar da shirye-shirye masu ɗaukar hankali ta hanyar manyan ayyukan gine-gine, shirye-shiryen tallafa wa matasa, da kuma sauye-sauye a fannonin noma, makamashi, ilimi da ƙere-ƙere.
Ministan ya bayyana cire tallafin fetur a matsayin ɗaya daga cikin manyan matakan da gwamnatin ta ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziki.
Ya ce: “Ɗaya daga cikin manya kuma mafi tasiri daga cikin matakan da wannan gwamnati ta ɗauka shi ne cire tallafin fetur, wanda ko da yake ya kasance mai raɗaɗi, amma sauyi ne da ya zama dole. Bayan ceton tattalin arzikin ƙasa daga rugujewa, wannan mataki ya hana ɓarna da asarar kuɗi sosai a tattalin arzikin mu.”
A cewar sa, kuɗaɗen da aka ceto daga cire tallafin ana amfani da su ne wajen manyan ayyukan raya ƙasa irin su hanyar Legas zuwa Kalaba, hanyar Sakkwato zuwa Badagiri, shimfiɗa layin dogo na Kaduna zuwa Kano, da sake gina hanyar mota ta Abuja zuwa Kaduna da Kano.
Ya ƙara da cewa akwai cigaba da aka samu wajen saka hannun jari a fannin ayyukan jin daɗi a faɗin ƙasar nan, tare da ƙaruwa a cikin kuɗaɗen da ake tura wa jihohi a kowane wata, wanda ke ba su damar aiwatar da ayyuka masu tasiri a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Dangane da shirye-shiryen tallafa wa jama’a, Idris ya bayyana cewa sama da ƙananan harkokin kasuwanci 900,000 sun riga sun amfana daga Shirin Tallafi da Lamunin Shugaban Ƙasa, yayin da sama da ɗalibai 350,000 suke amfana da lamunin karatu domin tabbatar da cewa babu matashin da zai kasa karatu sakamakon rashin kuɗi.
Ya bayyana cewa gwamnati ta ware kimanin naira biliyan 70 don lamunin karatu, wanda sama da matasa 600,000 suke neman amfana da shirin.
Ministan ya kuma bayyana ƙirƙirar Hukummomin Cigaban Yankuna a faɗin ƙasar nan da cewa wani mataki ne da Shugaban Ƙasa Tinubu ya ɗauka domin tabbatar da cigaba bisa yanayin kowane yanki daga cikin yankunan siyasa shida na ƙasar nan.
Ya ce aikin bututun gas ɗin Ajakuta zuwa Kaduna da Kano (AKK) yana tafiya yadda ya kamata, kuma zai bai wa masana’antu da ke kan wannan hanya wutar lantarki domin farfaɗo da masana’antu.
Ya ce: “Da zarar an kammala aikin, zai kawo wutar lantarki daga Ajakuta zuwa Kaduna da Kano. Wannan yana nufin cewa dukkan masana’antun da ke kan wannan layi za a farfaɗo da su.”
Idris ya bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin gwamnati mai ɗaukar rayuwar matasa da muhimmanci, inda ya ambaci shigar matasa da dama cikin Majalisar Zartarwa ta Tarayya a matsayin ministoci da kuma wasu muƙamai a hukumomin gwamnati.
Ya ƙara da cewa gwamnatin tana kashe naira biliyan 75 ta hanyar Bankin Masana’antu (BOI) domin tallafa wa ƙanana da matsakaitan masana’antu a fannoni daban-daban da nufin samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa matasa.
Ya ce: “Waɗannan ba wai wasu alƙaluma ne kawai marasa ma’ana ko maganganu na manufofi ba. Waɗannan damarmaki ne—damarmaki na zahiri, waɗanda za a iya auna su, ga kowane ɗan Nijeriya.”
Idris ya yi kira ga Kwamishinonin Yaɗa Labarai na jihohi da su ɗauki nauyin isar da saƙon da ya shafi manufofin gwamnati ga jama’a da kuma fahimtar yadda za su amfana da su.
Ya ce: “Saboda haka, nauyin mu ne a matsayin masu kula da yaɗa labarai, mu tabbatar da cewa ‘yan ƙasa a faɗin jihohin tarayya ba kawai sun san da waɗannan sauye-sauye da shirye-shirye ba ne, amma su ma fahimci yadda za su iya samun dama su amfana da su.”
Ya shawarci kwamishinonin da su koma jihohin su da sabon ƙwazo, su yi amfani da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da kuma haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki na cikin gida domin fassara shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya zuwa ayyuka masu amfani a matakin ƙasa.
Taron, wanda Gwamnatin Jihar Neja ta karɓi baƙuncin sa, ya haɗa kwamishinonin yaɗa labarai daga jihohin APC domin ƙarfafa dabarun sadarwa da kuma inganta haɗin gwiwa wajen aiwatar da Shirin Sabunta Fata a matakin jihohi da ƙananan hukumomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: shirye shirye
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Tana Cigaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi
Sojojin Sahayoniya suna ci gaba da yi wa mutane Gaza kisan kiyashi a kwana na 643 a jere.
Sojojin sahayoniyar suna amfani da dukkanin kayan yaki da su ka hada jiragen masa masu matuki da marasa matuki, da kuma manyan bindigogi.
Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare da tankokin yaki bayan kutsawarsu cikin yankin “Bi’irut-Turki” da “maslakh” dake kudancin Khan-Yunus. Tankokin sun rika bude wuta akan mai uwa da wabi da gidajen mutane a cikin yankin, da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da yawa.”
Majiyar Falasdinawa ta tabbatar da shahadar mutane 16, da su ka hada mata da kananan yara a wuruin da suke jiran karbar abincin agaji a shataletalen al-Dhayyarah, a Deir-Balah dake tsakiyar birnin Gaza.
A gabashin birnin Gaza kuwa, sojojin mamayar sun kara rusa gidaje masu yawa, da ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 4 a cikin iyalai guda na Abu Jild.
Har ila yau, majiyar ta ce, wani karamin yaro mai suna Yusuf Hassan al-Ammur ya yi shahada sanadiyyar raunukan da ya samu a jiya da ‘yan sahayoniyar su ka kai hare-haren da su ka kwantar da shahidai 4.
A sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” kuwa dake tsakiyar Gaza wani Bafalasdine mai suna; Abduljalil Khitab, da Akram al-Dairawi, sun yi shahada saboda harin da sojojin mamayar su ka kai wa motar da suke ciki. A tsakiyar daren jiya ma dai wasu Falasdinawan 5 su ka yi shahada a yankin Mawasi dake yammacin Khan-Yunus.