An wajabta wa ɗaliban firamare mallakar lambar NIN a Bauchi
Published: 22nd, July 2025 GMT
An wajabta wa ɗaliban makarantun firamare da Ƙaramar Sakandare mallakar lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) a Jihar Bauchi.
Hukumar Kula da Ilimin Bai-ɗaya a Matakin Farko ta jihar (SUBEB) ce ta bayar da umarnin ta hannun shugabanta, Alhaji Adamu Mohammed Duguri.
Ya bayyana cewa mallakar lambar NIN ta zama tilas lura da duk hukumomin shirya jarabawa da manyan makarantu suna amfani da ita kafin yi wa ɗalibai rajista.
Ya umarci shugabannin makarantun firamare da sakandare da su umarci ɗalibansu da su tabbata sun yi rajistar katin shaidar ɗan ƙasa sun mallaki lambar NIN kafin shekarar da za su zana jarabawar kammala makarantar da suke.
NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa A tsananta hukunci kan masu dukan mata — Sarki SanusiHaka zalika ya buƙaci da su tabbatar ’ya’yansu sun mallaki lambar NIN kafin su kai aji 6 na firamare zuwa aji 3 na Ƙaramar Sakandare domin guje wa makara.
Haka kuma ya umarci Sakatarorin Ilimi na ƙananan hukumomin jihar su tabbatar an bi wannan umarni sau da ƙafa domin guje wa fafar hira a ranar tafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai firamare ƙaramar sakandare Lambar NIN
এছাড়াও পড়ুন:
Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – Natasha
“Saboda barazanar tsaro da ke tattare da al’amuran siyasa, da kuma buƙatar kare lafiyata yayin gudanar da aiki, ina roƙon a dawo min da jami’an tsarona,” in ji ta.
Ta kuma haɗa da kwafin hukuncin kotun, inda ta jaddada marnin dawo da ita bakin aiki.
Sai dai komawarta majalisa ya haifar da ce-ce-ku-ce, domin Majalisar Dattawa ta ce hukuncin kotun da Sanata Natasha ke dogaro da shi ba dole ba ne a aiwatar da shi, domin ba umarni ba ne kai-tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp