Aragchi: Kofar Iran Ta Tattaunawa A Bude Take, Amma Amurka Sai Ta Biya Kudade Kan Kura-Kuranta
Published: 11th, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar tattaunawa da Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya a bude take, amma kafin haka sai gwamnatin kasar Amurka ta biya diyyar kura kuran da ta yi a bayan.
A wata hirar da yayi da Jaridar Le Monde na kasar Faransa Aragchi ya kara da cewa da farko Amurka yakamata ta canza halayenta, na rashin kaiwa kasar Iran hare-hare a lokacin tattaunawa.
Ya ce diblomasiyya hanyace mai tituna biyu na zuwa da komawa, amma Trump ya zo ya rufe dayar. Kuma tattaunawar diblomasiyya a wajen Iran a ko yauce a bude yake, Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Iran a cikin yakin kwanaki 12 keta hurumin diblomasiyya ne, kuma dole Amurka ta biya diyyan Barnan da ta yi. Kuma wannan hakkin Iran ta nemi wannan hakkin.
Hakama kaiwa cibiyan makamashin Nukliya wanda ke karkashin kula na hukumar IAEA kuskure ne. don babu tabbaci daga hukumar kan cewa shirin ya karkata daga na zaman lafiya. Wannan ma sai Amurka ta biyya diyyar yin haka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Najeriya ta casa Jamhuriyar Benin 4-0
Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta.
Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa. A gaba kuma, an hada Victor Osimhen da Akor Adams domin tayar da kura.
Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika masa. Cheetahs sun yi kokarin farkeaw a minti na 12, amma Calvin Bassey ya dakile harin.
Na yafe wa Maryam Sanda —Mahaifin Bilyaminu Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya AbdullahiA minti na 22, Osimhen ya kusa kara ci, amma dan wasan baya na Benin ya hana shi. Sai dai a minti na 38, Chukwueze ya sake aika masa da wata kwallo, kuma Osimhen bai yi wata-wata ba — ya zura ta biyu! Najeriya 2, Benin 0.
Bayan hutun rabin lokaci, Benin sun fara da matsa lamba, amma Osimhen ya sake daukar hankalin duniya — inda a minti na 51, ya cika hat-trick dinsa! Kwallo ta uku ke nan a hannunsa.
Super Eagles sun ci gaba da matsa lamba, inda suka nemi ci na hudu a minti na 68, amma Ndidi ya kasa cin kwallon da aka buga masa.
A minti na 90 Onyeka ya zura wa Super Eagles kwallon Najeriya na hudu a ragar Jamhuriyar Benin.
Wannan wasan ya nuna cewa Osimhen ba dan wasa bane kawai — jarumi ne, gwarzo ne, kuma jagora ne a fagen kwallon kafa.
Najeriya na kan gaba a wannan fafatawa, kuma alamu na nuna cewa Super Eagles na kan hanya madaidaiciya zuwa Kofin Duniya ta 2026.