“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.”

“Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!”

A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing.

A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar Sin, tare da hada kai da kasar Sin da ma sauran baki ’yan kasuwa wajen kyautata tsarin samar da kayayyaki na duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: samar da kayayyaki na

এছাড়াও পড়ুন:

Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, da shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Huning, sun gana da shugaban majalisar dattijan kasar Madagascar Richard Ravalomanana.

Yayin ganawar, Zhao Leji ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin kokari tare da Madagascar, don sa kaimi ga raya hadin gwiwa, da sada zumunta a tsakaninsu, da samar da gudummawa ga raya kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamani. Kana yana fatan hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu, za su kara yin mu’amala, da hadin gwiwa da juna, don taimakawa wajen raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Madagascar a dukkan fannoni.

Yayin ganawar tsakanin Wang Huning da Ravalomanana, Wang ya bayyana cewa, Sin da Madagascar hakikanin abokan juna ne, yayin da ake zamanintar da kasashen. Kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, na fatan yin mu’amala tare da majalisar dattijai ta kasar Madagascar, wajen taimakawa raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, Ravalomanana ya bayyana cewa, majalisar dattijan kasar Madagascar, na fatan yin kokari tare da kasar Sin, wajen inganta mu’amala a tsakanin hukumomin kafa dokokin kasashen biyu, don sa kaimi ga raya hadin gwiwar kasashen biyu, a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, da harkokin kananan hukumomi kasar da sauransu. Kana yana fatan kara yin mu’amala da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, a fannin sarrafa harkokin kasa, da kuma sa kaimi ga daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
  • Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
  • Karin Maganar Sinawa: Koyar Da Su Ya Fi Bayar Da Kifi
  • Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana
  • Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati 
  • Kamfanonin lantarki ya zu katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati 
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Shirin Ba Da Horo A Kasar Sin Ya Taimaka Wa Inganta Masana’antar Gyadar Senegal
  • Gwamnatin Kano Ta Maida Gidan Marayu Zuwa Cibiyar Gyaran Mata Masu Shaye