Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
Published: 22nd, July 2025 GMT
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, tare da wasu mutane goma sha biyu na samun kulawa a asibiti bayan tsira daga wani hadarin mota da ya faru a kan hanyar Katsina zuwa Daura, a Jihar Katsina.
Hatsarin ya faru ne sakamakon taho-mu-gama da wata motar haya kirar Volkswagen a kusa da Tashar Motoci ta KTSTA da ke Daura.
Duk da cewa hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ba ta fitar da sanarwar hukumance dangane da lamarin ba, shaidu da hotunan da aka dauka daga wurin sun tabbatar da cewa motocin biyu sun lalace matuka.
Shaidun gani da ido sun shaida wa Radio Nigeria cewa motar gwamnan ba ta cikin sahun motocin rakiyar gwamnati a lokacin da hadarin ya faru.
Daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen daukar wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Tarayya na Daura, ya shaida wa Radiyon Najeriya cewa dukkan fasinjoji tara da ke cikin motar hayar sun samu raunuka.
“Mun kai su Asibitin Gwamnati na Daura inda ake kula da su yanzu,” in ji shi.
A halin yanzu, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Katsina, Alhaji Bala Salisu Zango, ya ziyarci fasinjojin motar hayar da suka jikkata a Asibitin Gwamnati na Daura, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin dukkan kudin maganinsu.
Bakwai daga cikinsu sun samu raunuka kadan ne kawai, yayin da biyu kuma suka sami karaya.
“Gwamnatin Jihar Katsina za ta biya dukkan kudin maganinsu kuma za ta ci gaba da kula da lafiyarsu har sai sun warke.” in ji Zango.
Ya kara da cewa gwamnan ma yana cikin koshin lafiya, kuma tuni aka sallame shi daga Asibitin Tarayya na Daura.
“Na yi magana da shi ta waya ba da dadewa ba, yana cikin koshin lafiya. An kwantar da shi tare da sauran wadanda suka jikkata a Asibitin Tarayya na Daura, kuma an sallame shi bayan an tabbatar da cewa lafiyarsa ta daidaita.”
Haka kuma, wata sanarwa da Sakataren Watsa Labarai na Gwamna Radda, Malam Kaula Mohammed ya sanya wa hannu ta tabbatar da cewa gwamnan yana cikin koshin lafiya.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, gwamnan ya bayyana cewa shi da sauran wadanda hatsarin ya rutsa da su suna cigaba da samun kulawa.
Daga Isma’il Adamu.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamna Hadarin Mota Jihar Katsina
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Kame ‘Yan Gwagwarmaya Da Hukumar Falasdinawa Ke Yi
Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila
Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da Jenin, da kwace makamansu, da kuma ci gaba da fatattakar ‘yan gwagwarmaya a duk fadin yankin gabar yammacin kogin Jordan, yana nuni da ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila ce da murkushe al’ummar Falastinu.
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Shadid ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Kamen da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa suka yi kan ‘yan gwagwarmaya da kuma fitattun al’umma da masanan Falasdinawa, biyan ladar moro-maron yahudawan sahayoniyya ne da jami’an hukumar Falasdinu suka ci.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ruguza gidajen mutane a Jenin, tare da koran dubban mutane a Tulkarm, ana kuma kwace yankunan mutane a gabar yammacin kogin Jordan.
Shadid ya bayyana cewa: Wadannan ayyuka suna nuna manufar Hukumar Cin gashin Falasdinawa ne na ganin ta raba ‘yan gwagwarmaya da yankin gabas yammacin kogin Jordan, tare da barin Falasdinu a bude ga sojojin mamayar Isra’ila gungun ‘yan ta’addan su aiwatar da tsare-tsaren Sanya Falasdinawa gudun hijira.