Danbun Shinkafa Da Nama Da Kifi
Published: 12th, July 2025 GMT
Yadda ake hadawa:
Da farko za ki gyara shinkafarki ki wanke ta ki tsane ta sai ki bar ta ta dan bushe, sannan a barzo miki ita a inji sai ki ajiye a gefe.
Sai ki wanke namanki ki dora a wuta ki sa maggi, da gishiri da tafarnuwa da citta da albasa. Sannan sai ki zo ki tankade wannan shinkafar da kika barzo ta saboda da tsakin ake amfani.
Sai ki sa ruwa ki wanke tsakin ki tsane shi, sai ki zuba shi a madambaci ki dora a wuta.
Sai kuma ki gyara zogalenki, ki wanke, ki hada da tsakin sai ki rufe.
Ki tsame namanki, ki yanka kayan miyanki ko ki jajjaga duk daya ne ki ajiye a gefe.
Uwargida sai ki duba tsakinki idan ya yi za ki ji yana kamshi shi ne tsakin ya dahu.
Sannan ki sauke ki zuba a roba mai fadi, sai ki zuba soyayyen man da albasa da sauran kayan miya wanda dama kin soya su sai maggi, da gishiri, da kori, da tafarnuwa duk ki zuba sai tare da kifin wanda dama kin gyara shi ki juya ki daddanna sosai saboda komai ya yi dai-dai kar wani waje ya fi wani waje dandano.
Sai ki zuba dan ruwan tafasasshen naman ki juye a tukunya ki maida shi wuta ki bashi kamar minti sha biyar, za ki ji gida ya dau kamshin dadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA