Aminiya:
2025-11-03@07:22:17 GMT

’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano

Published: 10th, July 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, sata, zamba da kuma tayar da hankalin jama’a.

An kama waɗannan mutane ne ƙarƙashin sabon samamen da rundunar ta ƙaddamar mai suna “Operation Kukan Kura” wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, 2025.

Kotun ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin gwamnan Edo Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Alhamis.

Ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin daƙile aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya a faɗin Jihar Kano.

Ya ce samamen ya samu goyon bayan Sufetan Janar na ’Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, domin ƙarfafa haɗin kai da al’umma wajen yaƙi da laifuka.

Kwamishinan, ya bayyana cewa wannan aiki yana bin tsarin aikin rundunar, wanda ke nufin haɗa kai da al’umma wajen hana aikata laifuka.

Rundunar ta nazarci halin tsaro a jihar tare da duba yankunan da laifuka suka fi yawa kafin ta ƙaddamar da samamen.

Ya ce babban burin wannan aiki shi ne zama tamkar wata hanyar gargaɗi domin gano da kuma daƙile barazanar laifuka tun kafin su faru.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai mutum 21 da ake zargi da fashi da makami, huɗu ana zargin su da garkuwa da mutane, biyar kan safarar miyagun ƙwayoyi.

Sauran sun haɗa da mutum 12 da ake zargi da satar motoci, huɗu ana zargin su da zamba, sai wasu biyar da ake zargi da sata, da kuma mutum 47 da ake zargi da tayar da hankalin jama’a.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da motoci guda shida, adaidaita sahu guda takwas, babura guda tara, tabar wiwi, kwalabe 86 na kayan maye, takubba 16 da wuƙaƙe.

Kwamishinan, ya ce waɗannan nasarori za a ci gaba da amfani da su wajen inganta dabarun aiki da rundunar ke aiwatarwa.

Ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Ɓata gari da ake zargi da

এছাড়াও পড়ুন:

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matar aure ta yanka wuyan mijinta, ta fasa masa ido da wuƙa a Neja
  • Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m